Home Back

Abubuwan Da Ke Rusa Masana’antun Kiwon Kaji A Nijeriya

leadership.ng 2024/5/15
kiwon kaji

Ga duk wanda yake son samun cin nasara a kiwon kajin gidan gona, wajibi ne ya kiyaye tare da gujewa wasu kurakurai.

Rashin kiyaye wadannan kura-kurai ne ke sanya wa wasu masu sana’ar ba sa iya kai bantansu a cikin wannan sana’a. Ga dai wasu dalilai biyar da ke jawo wa wannan masana’anta barazanar durkushewa, idan har mai sana’ar bai kiyaye wadannan ka’idoji ba kamar haka:

  1.  Rashin Gudanar Da Bincike: Akasarin masu fara yin kiwon kajin gidan gona ba sa gudanar da kwakkwaran bincike a kan wannan harka, duk kuwa da cewa ita ma tamkar sauran irin sana’oi ce da ke bukatar gudanar da bincike kafin a fara aiwatar da ita.
  2. Samar Da Ingantaccen Tsarin Dakunan Kwanan Kajin:
    Mafi akasarin masu kiwon kajin gidan gona, ba sa samar musu da wadatattun dakunan kwana, inda hakan ke sanya su kasancewa cikin cinkoso, wanda hakan ke kai su ga kamuwa da cututtuka ko fuskantar gagarumar matsala.
  3. Samun Kyakkyawan Horo: Ga duk wanda zai shiga wannan sana’a ta kiwon kaji, akwai bukatar samun kyakkyawan horo kan yadda ake yin kiwon, wanda ba sai lallai wanda ya samu takardar shedar Difloma ba.
  4. Tsadar Kayan Abicin Kajin: Samun hauhawar farashin abincin kajin gidan gona, wanda hakan ke haifar wa da masu kiwon gazawa wajen ci gaba da kula da kajin nasu. Kajin gidan gonar na kai wa daga kwana 33 zuwa 42, wanda har sai sun kai nauyin kilo 2.8 zuwa kilo 3.
  5. Rashin Tsarin Kasuwanci Mai Kyau: Rashin samar da kyakkawan tsarin kasuwanci, na haifar wa da masu wannan sana’a gagarumar matsala, wanda hakan ke sanadiyyar fadawar masu sana’ar hannun ‘yan na kama da ke sayen kajin cikin farashi mai sauki, su kuma su sayar a kan farashi mai tsada.
People are also reading