Home Back

Tattaunawar DW da Felix Tshisekedi

dw.com 2024/5/17
Felix Tshisekedi a hirarasa da tashar DW
Felix Tshisekedi a hirarasa da tashar DW

 Bude kofofiga abokan hulda na ketare don bukasa tattali arziki, da shawo kan matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa da kuma sarafa dumbin ma'adinan karkashin kasa da Allah ya huwace wa Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango don inganta rayuwar al'umma, kadan ne daga alkawaran da shugaba Felix Tschisekedi ya dauka a lokacin da yake zawarcin kuri'un 'yan kasar domin samun wa'adin mulki a karo na biyu. Watanni hudu bayan zarcewa kan gadon mulkin kasar da ke gabashi Afrika mai fama da manyan kalubale, Tschisekedi na kokarin tabbatar da wannan manufa ta hanyar shiga lungu da sako da nufin janyo hankali amintattun abokan hulda. A zantawarsa da DW shugaba Tschikedi ya bayyana Jamus a matsayin kasar da ta dace domin kulla alaka mai aminci da ita a fannoni daban-daban na ci gaba musanman ma makamashi, inda ya ce ya yi imani kasashen biyu za su  ribanta sosai.

Kwango na da tarin arizikin ma'adinai da duniya ke bukata

 ''Allah ya albarkaci Kwango da dumbin arziki. Abin da ya rage shine sallamowar masu saka hannu jari don sarrafa wadannan albarkatu. Fannin samar da  makamashi na a sahun farko na fannin da zan bukaci Jamus ta saka hannun jari domin a bunkasashi, kana daga bisani sai fannonin ilimi da kiwon lafiya da noma da ke da matukar mahimmanci a wannan lokaci. Baya ga haka sai kuma fannin sadarwa da kimiyar zamani da matasanmu suka fara raja'a kai.''

Matsalar rashin tsaro da tawaye sun hana Kwango ci gaba

Sai dai matsalar tsaro mai nasaba da kungiyoyin masu dauke da makamai da kuma 'yan tawayen M23 masu samun goyoyon bayan Ruwanda da suka sukuni a yankunan kasar masu arzikin ma'adinai, na zama babban kalubale ga gwamnatin Kinshassa. Ana ma fargabar wannan rikici ya haifar da barkewar yaki tsakanin kasashen biyu makwabta da ke wa juna kallon hadarin kaji. To amma a tambayi shugaba Tschisekedi ko zai gana nan zuwa gaba da takwaransa   Paul Kagamedon warware wannan dambarwa?

People are also reading