An Dauki Mataki Kan Dan Sandan da Aka Nadi Bidiyonsa Ya Na Karbar ‘Na Goro’ a Imo
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Imo - Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta ce ta dauki mataki kan jami’anta mai suna Sifeta Isong Osudueh da aka nadi bidiyonsa yana karbar cin hanci.
Rundunar ta ce ta rage wa Sifeta Isong matsayi saboda karbar 'na goro' hannu masu ababen hawa a kan hanyar Owerri zuwa Onitsha.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Henry Okoye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bidiyon da ya bazu a ranar Litinin, ya nuna jami’in yana karbar kudi daga hannun direbobin da ke wucewa ta titin daya ke gudanar da bincike.
Ana kuma iya ganin shi yana mika canji ga wasu direbobin a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
A cewar sanarwar, an ragewa Osudueh, wanda ke aiki a sashin yaki da ta’addanci a Owerri matsayi bayan ya fuskanci hukuncin ladabtarwa.
A lokaci guda kuma, an baiwa jami'in da ke sa ido kan dan sandan takardar tuhuma sahoda rashin kulawa da da'ar jami'an da ke karkashinsa.
Wani mutum mai suna @ChuksEricE ne ya wallafa bidiyon dan sandan yana karbar 'na goro' a shafinsa na X.
Kalli bidiyon a kasa:
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun jihar Kano ta ba 'yan sanda umarnin fitar da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga fadar Nassarawa.
Haka zalika, kotun ta dakatar da tsofaffin sarakunan Kano biyar daga bayyana kansu a matsayin sarakuna biyo bayan karar da gwamnatin jihar ta shigar a kotun.
Asali: Legit.ng