Home Back

Kano: Hakimai da Ciyamomin Kananan Hukumomi 44 Sun Ziyarci Sanusi II, Fada Ta Cika Maƙil

legit.ng 2024/7/3
  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya karbi hakimai da shugabannin ƙananan hukumomi 44 a jihar Kano
  • Hakiman da shugabannin riko na kananan hukumomin sun kawo caffan ban girma ne ga Sarkin a yau Juma'a 31 ga watan Mayu
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba dambarwa kan sahihin sarki a jihar Kano bayan tube sarkin na 15, Aminu Ado Bayero

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Hakimai da shugabanni riko na kananan hukumomi 44 a jihar Kano sun kai ziyara ga Muhammadu Sanusi II.

Hakiman da shugabannin kananan hukumomin sun kai caffan ban girma ga Sarkin Kano na 16 domin nuna goyon baya.

Daily Nigerian ta tattaro cewa hakiman sun kai ziyarar a yau Juma'a 31 ga watan Mayu a fadarsa.

Wata majiya ta tabbatar da cewa duka hakiman sun taho da dagatansu a ƙauyuka domin yin mubaya'a ga sabon Sarkin.

Har ila yau, an tabbatar su ma shugabannin ƙananan hukumomin sun zo da duka kansilolinsu zuwa fadar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daukacin hakimai da shugabannin riko na kananan hukumomi 44 sun kawo caffan ban girma ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II."
"Hakiman sun zo da dagatai daga kauyukansu yayin da shugabannin suka zo da kansilolinsu da sauran mambobi."
"Yau fadar ta cika makil, inda suka tabbatar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano."

- Cewar majiyar

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading