Home Back

Ana Shagalin Sallah, Bola Tinubu Ya Fara Samun Goyon Baya Game da Takara a 2027

legit.ng 2024/7/3
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fara samun goyon baya daga shugabannin siyasa gabanin babban zaɓen 2027
  • Jagororin jam'iyyar APC a shiyyar Kudu maso Kudu sun bukaci Tinubu ya sake neman takara karo na biyu a zaɓe mai zuwa
  • A cewarsu, sun aminta da salo shugabanci da tsare-tsaren da gwamnatinsa ta zo da su da nufin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River - Jam’iyyar All Progressive Congress(APC) a yankin Kudu-maso-Kudu ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin APC na Kudu maso Kudu suka fitar bayan wani taro da suka yi a Kalaba, jihar Kuros Riba ranar Lahadi.

Bola Ahmed Tinubu.
APC reshen Kudu masu Kudu ta amince Tinubu ya yi tazarce a 2027 Hoto: Dolusegun Asali: Facebook

Sun yabawa shugaban ƙasar bisa tsare-tsare, ayyuka da shirye-shiryen da ya zo da su bayan hawansa mulki, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsu, waɗannan tsare-tsaren tattalin arziki da Bola Tinubu ya ɗauka za su mayar da ƙasar nan kan turba mai kyau.

Shugabannin sun kara jaddada goyon bayansu ga tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu a ɓangarorin shugabanci, tattalin arziki, tsaron ƙasa da ayyukan more rayuwa.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Tinubu ya ayyana kawo karshen tallafin man fetur, matakin da ya kawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya zuwa kashi 33.95 a watan.

Bayanai sun nuna cewa a rahoton shekara-shekara, hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru da kashi 11.54% idan aka kwatanta da na watan Mayun 2023 kashi 22.41%.

Amma duk da haka shugabannin APC na shiyyar Kudu maso Kudu sun yabawa shugaban kasa bisa jajircewa kan aikin hanyar gabar teku, da kuma fara aikin ta kowane ɓangare.

Bugu da ƙari, sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio a matsayin jagoran jam'iyyar APC shiyyar Kudu maso Kudu.

Gwamnatin Tinubu ta kare kanta

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta yi martani ga labarin da wata jarida a kasar waje ta wallafa na cewa kasar nan na fuskantar mafi munin tabarbarwar tattalin arziki a tarihinta.

Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kafafen yada labarai, Bayo Onanuga ya dora laifin matsalolin da ake fuskanta kan gwamnatocin baya da gwamnatinsu ta gada.

Asali: Legit.ng

People are also reading