Home Back

PSG Na Neman Dauko Lamine Yamal Daga Barcelona A Kan Yuro Miliyan 200

leadership.ng 2024/5/4
PSG Na Neman Dauko Lamine Yamal Daga Barcelona A Kan Yuro Miliyan 200

Ƙungiyar kwallon kafa ta PSG na neman daukar dan wasan Barcelona, Lamine Yamal a kan kudi Yuro Miliyan 200.

PSG na neman wanda zai maye mata gurbin dan wasanta, Klylian Mbappe idan ya bar kungiyar inda ake alakanta shi da komawa Real Madrid, a karshen kakar wasa ta bana.

Goal ta bayyana cewar akwai kyakkyawar alaka tsakanin daraktan wasanni na PSG, Luis Campos da wakilin Yamine Yamal, Jorge Mendes wanda ake hasashen hakan zai iya saukaka wa Le Perisien wajen daukar matashin.

People are also reading