Home Back

Macron ya zargi IS game da harin Rasha

dw.com 2024/5/15
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce duk alamu sun nuna cewa tsagerun kungiyar IS suka kai hari a wajen kidar Gala a birnin Moscow fadar gwamnatin Rasha inda kusan mutane 140 suka halaka a kasrhen mako, kuma duk wani yunkurin mayar da lamarin kan kasar Ukraine ba zai haifar da alheri ga kasar ta Rasha ba. Shugaban na Faransa ya ce duk bayanan suke da shi na asiri sun nuna cewa mayakan IS suke da alhakin harin na Rasha.

Ita dai kasar ta Rasha tun farko ta yi watsi da batun Amirka da wasu kasashe cewa tsagerun kungiyar IS masu kaifin kishin Islama suka kai harin na karshen mako, maimakon haka kasar ta Rasha tana danganta lamarin da yakin da ke faruwa bayan kutsen da ta kaddamar kan kasar Ukraine. Tuni Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce akwai wasu daga bangaren Ukraine da suka shirya tabar maharan, abin da kuma mahukuntan Ukraine suka musanta.

People are also reading