Home Back

An yi waje da Mexico a Copa America na bana

bbc.com 2024/10/6
Copa America

Asalin hoton, Reuters

Ecuador ta tashi 0-0 da Mexico ta kuma yi ta biyu a cikin rukuni a Copa America, za ta buga kwata fainal da mai rike da kofin Argentina.

Da wannan sakamakon an yi waje da Mexico a gasar, bayan da ta kare a mataki na uku a rukuni na biyu, inda Ecuador ce ta yi ta biyu da rarar ƙwallaye.

Mexico ta saka matsi daf da za a tashi a wasan har ta kai ga samun fenariti a karin minti bakwai, bayan da Felix Torres ya girbe Guillermo Martinez.

To sai dai VAR ta bukaci alkalin wasa da ya je ya kalli abinda ya faru, inda aka fayyace cewar Torres ya taɓa kwallon kafin ya yi girben.

Ecuador za ta fafata da Argentina ranar Juma'a 5 ga watan Yuli.

Venezuela ce ta yi ta ɗaya a rukuni na biyun, bayan da ta doke Jamaica 3-0, za kuma ta fuskanci Canada ranar Asabar 6 ga watan Yuli a daf da na kusa da na karshe.

Wadanda suka ci wa Venezuela ƙwallayen sun hada da Eduard Bello da Salomon Rondon da kuma Eric Ramirez.

Haka kuma tawagar ta doke Ecuador da Mexico a fafatawar cikin rukuni na biyun.

People are also reading