Home Back

Ana Tsaka da Kuka da Mulkin APC, ’Yan Majalisa 3 a Arewa Sun Sauya Sheka Zuwa Daga PDP

legit.ng 2024/8/24
  • Wasu 'yan majalisa sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a jihar Kebbi tare da gomman mabiyansu
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake kuka kan yadda APC ke tafiyar da gwamnati a matakin kasa
  • Ba sabon abu bane a samu jihohin da babu 'yan jam'iyyun adawa a majalisun jiha, haka kan ga kantoma na kananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya karbi dandazon ‘yan jam’iyyar PDP sama da 100 da suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Gwamnan ya kuma yi farin ciki da karbar wasu jiga-jigan PDP, ciki har da ‘yan majalisa uku zuwa jam’iyyar ta APC.

Ya karbi bakuncin wadannan masu sauya sheka ne a gidan gwamnatin jihar da Birnin Kebbi, ya kuma yi alkawarin ba zai nuna masu wariya ba.

Jiga-jigan PDP sun koma APC a Kebbi
Yadda 'yan siyasar Kebbi suka koma APC | Hoto: Muhammad Idris Bunza Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi, gwamnan ya bayyana gwarin gwiwarsa na yadda yake tafiyar lamurran mulki da raba romon dimokradiyya a jihar, TVC News ta ruwaito.

Gwamna ya karbi sabbin tuba dag PDP zuwa APC

Gwamna Idris ya kuma kara da cewa, sabbin ‘yan jam’iyyar tabbas za su kawo ci gaba da kuma tasiri mai kyau ga jam’iyyar APC.

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abubakar Kana-Zuru ya bayyana jin dadinsa da samun sabbin mambobi a jam’iyyar da yake shugabanta.

Ya kuma bayyana shirin da jam’iyyar ke dashi ga dukkan mambobinta sabbi da tsoffi a yanzu da nan gaba.

Manyan wadanda suka sauya sheka zuwa APC

Tsohon sakataren dindindin na ma’aikatar ayyukan jihar kuma tsohon jigon APC daga karamar hukumar Bunza, Alhaji Sani Bunza ya yi magana kan dalilin da yasa dandazon jama’ar suka yanke komawa APC.

Wasu daga cikin jiga-jigan da suka shiga APC sun hada da Alhaji Faruku Ajala, Alhaji Bala Gradee, Hon. Garba Hassan Wara, Hon. Bello Shehu Kasaura, Alhaji Umar Yaro Gari da Hon. Umaru Kambaza.

Ana ci gaba da kuka da jam’iyyar APC a matakin kasa, duk da haka ana ci gaba da shiga jam’iyya a bangarori daban-daban.

Dan majalisa ya koma APC

A wnai labarin kuma, tsohon dan majalisar wakilan tarayya a mazabar Amuwo Odofin, Hon Oghene Egoh, ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC a jihar Legas.

Egoh dai ya bar PDP ne da mafi yawan shugabannin jam'iyya na Amuwo Odofin, da dumbin magoya bayansa, duk sun rungumi APC.

Tsohon dan majalisar ya ce tsare-tsaren shugaban kasa Bola Tinubu da ayyukan alherin Babajide Sanwo-Olu ne suka jawo hankalinsa zuwa APC, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

People are also reading