Home Back

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya Gana da Likitoci Masu Yajin Aiki, ya Ɗauki Alƙawarin Gyara

legit.ng 2024/6/29
  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya tattauna da kungiyar likitoci ta ƙasa (NMA) da takwararta ta masu aiki a asibitocin gwamanti da kwararru likitocin haƙori a yau
  • Tattaunawar ta biyo bayan yajin aiki da likitocin su ka tsunduma saboda barazana da wasu jami'an tsaro su yi wa likitocin yara a asibitin Hasiya Bayero
  • Abba Gida-gida ya hakurkurtar da likitocin tare da ba su baki kan su koma bakin aiki, sannan gwamnan ya ɗauki alƙawarin za a duba damuwar da su ke da su domin gyara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Kano- Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya gana da ƙungiyar likitoci ta ƙasa (NMA) reshen jihar bayan sun tsunduma yajin aiki.

Gwamnan ya umarci likitocin da su ka dakatar da aiki a asibitin yara na Hasiya Bayero da su koma bakin aikin ceton rai da su ke yi.

Jihar Kano
Yajin Aiki: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tattauna da likitoci, an cimma matsaya Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa Asali: Facebook

Gwamna Abba ya fitar da jawabi

A sanarwar da darakta janar kan yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na facebook, ya ce ƙungiyar da gwamnatin Kano sun samu fahimtar juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zaman da aka yi tsakanin kungiyar NMA da ta likitocin haƙori da ke aiki a asibitocin gwamanti NAGMMDP, an cimma matsaya kan koken jami'an lafiyar. Daga abubuwan da aka tattauna a taron akwai batun walwalar likitoci da tsaron rai da lafiyarsu a wurin aiki.

Kano focus ta wallafa cewa gwamnan ya yi takaicin yadda jami'an tsaro su ka kutsa kai asibitin Hasiya Bayero da makamai tare da tsorata likitocin da ke aiki. Ya ce bai kamata jami'an tsaro su rika fitar da makamai cikin al'umma ba tare da wani dalili ba.

NMA ta janye kanta daga yajin aiki

A baya mun kawo muku labarin cewa ƙungiyar likitoci ta NMA reshen jihar Kano ta barranta kanta daga yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta kira.

Sakataren ƙungiyar, Dr. AbdulRahman Ali ya ce su kungiya ce ta ƙwararru kuma masu zaman kansu, saboda haka 'ya 'yansu sun fito aiki.

Asali: Legit.ng

People are also reading