Home Back

Ina So A Gurfanar Da Ni A Kogi – Yahaya Bello

leadership.ng 4 days ago
Gwamnatin Kogi Za Ta Fara Hukunta Duk Wanda Ya Ki Karbar Tsoffin Kudi

Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume 19, ya aike wa babban alkalin babbar kotun tarayya, Mai shari’a John Tsoho, yana neman a ba shi damar ya fuskanci shari’a a Kogi.

Tsohon gwamnan, a cikin wasikar da ya rubuta ta hannun lauyoyinsa karkashin jagorancin Mista Abdulwahab Mohammed SAN, ya bayyana cewa babbar kotun Lokoja ce kadai ke da hurumin sauraron tuhumar da EFCC ke masa.

Sai dai har yanzu ya kasa gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, domin ci gaba da sauraron karar tuhumar da ake masa, inda lauyansa Mista Adeola Adedipe SAN, ya shaida wa mai shari’a Emeka Nwite, wasikar da wanda yake karewa ya rubuta wa kotun cikin jawabinsa.

A nasa bangaren, lauyan EFCC Mista Kemi Pinhero SAN, ya bukaci kotun da ta tilasta wa lauyan wanda ake kara ya bayyana dalilin da ya sa wanda yake karewa ba ya zuwa kotu.

Ya ce duk da alƙawarin da ya dauka a ranar 13 ga watan Yuni na tabbatar da kasancewarsa a gaban kotu, tare da kiran kotu da ta yi watsi da bukatar wanda ake karewa.

Bello, wanda ya mulki Jihar Kogi tsawon shekaru takwas, yana fuskantar tuhuma kan zargin karkatar da kuɗaɗe da cin amana da almubazzaranci da dukiyar al’umma da ta kai Naira biliyan 80.

EFCC ta yi zargin cewa tsohon gwamnan tare da dan uwansa Ali Bello da wasu mutane biyu, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu, suna da hannu wajen karkatar da kuɗaɗen.

People are also reading