Home Back

Yadda mahara suka buɗe wa motocin alfarma wuta, suka yi samamen masu motocin cikin dajin Shagamu

premiumtimesng.com 2024/5/19
MATSALAR TSARO A KATSINA: ‘Yan bindiga sanye da hijabi sun sake afka wa jami’an tsaro a yankin Batsari

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun sun tabbatar da cewa mahara sun tare matafiya kan hanyar Shagamu zuwa Benin, inda suka sauke lodin masu zanga-zangan motocin alfarma, suka nausa da su cikin daji.

Lamarin wanda ya faru tsakanin Ilisan/Iperu, kamar yadda Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Omolola Odutola ta bayyana wa manema labarai, a Abeokuta, ta ce an yi garkuwa da mutanen ne a ranar Juma’a.

Sai dai ta ce har yanzu ‘yan sanda ba su tantance adadin yawan mutanen da aka arce da su ba.

Ta ce maharan sun kashe mutum ɗaya daga cikin matafiyan, kuma ba akai ga gane ko wane ne suka kashe ɗin ba.

Ta ce lamarin ya faru a ranar Juma’a, wajen ƙarfe 6:55 na yamma.

Kuma ta ce an fahimci harin na fashi da makami ne, kisa da kuma garkuwa da mutane.

“Mun samu rahoton cewa kamar mutum bakwai ne ɗauke da bindiga samfurin AK 47 suka tare hanyar Shagamu zuwa Benin.

“Lokacin da DPO na Ilisan ya isa wurin ya taras da an ratattaka wa motoci biyu masu alfarma harsasai.

“Akwai wata Lexus Jeep 300 mai lamba LND 640 DY, wadda sunan direban ta Chilaka Lugard.

Akwai wata Lexus Jeep 350, mai lamba LSR 996 JF mallakar wani mai suna Kingsley Chineme.

“A cikin Lexus 350, an samu jaka da kuɗi a cikin ta Naira 113,000, iPhone 6 da iPhone 11 Promax.

“Sannan kuma an samu gawar wani mutum wanda aka harba a kai.

“Mota ta uku kuwa an yi mata lodin filanten, kuma direban na cikin waɗanda aka arce da su, amma ya kuɓuta, an bar shi ya tafi da motar sa da lodin filanten ɗin sa.”

Sauran motoci Lexus kuma an tafi da su Ofishin DPO na Ilisan,” inji Kakakin ‘Yan Sanda.

Ta ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Ogun, Abiodun Alamutu, ya kira taron gaggawa inda ya umarci zaratan jami’ai su afka cikin daji domin ceto waɗanda aka yi garkuwar da su.

Ta ce shi ma Kwamishinan ‘Yan Sandan ya ziyarci wurin da abin ya faru.

People are also reading