Home Back

'Yan Kwadago Sun Sake Fatali da Sabon Mafi Karancin Albashi, Sun Fadi Abin da Za a Biya

legit.ng 2024/7/2

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta sake yin watsi da sabon mafi ƙarancin albashin da gwamnatin tarayya ta gabatar.

A wannan karon, ƙungiyoyin ƙwadago da suka haɗa da NLC da TUC sun yi watsi da tayin gwamnatin tarayya na biyan N60,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

'Yan kwadago sun yi fatali da sabon mafi karancin albashi
Kungiyoyin kwadago sun yi watsi da N60,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, NLC Headquarters Asali: Facebook

A halin da ake ciki, ƙungiyar ƙwadago ta kuma sauya matsayinta daga N497,000 a makon da ya gabata zuwa N494,000.

Wani mamba a kwamitin tattaunawa kan batun ƙarin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Najeriya ya bayyana hakan ga wakilan tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa wakilan gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu a taron, sun gabatar da mafi ƙarancin albashi na N60,000 a duk wata saɓanin N57,000 da suka gabatar a makon da ya gabata.

Tun da farko dai gwamnati ta gabatar da N48,000 da kuma N54,000 a makon da ya gabata a matsayin mafi ƙarancin albashi, yayin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da su.

Ƙungiyar kwadago ta kuma gabatar da N615,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi amma daga baya ta janye buƙatar zuwa N497,000 a makon jiya sannan zuwa N494,000 a ranar Talata (yau).

Har yanzu dai kwamitin tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan bai cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashin da za a riƙa biyan ma’aikatan ba.

Yanzu dai saura kusan kwanaki uku wa’adin ranar 31 ga watan Mayu da ƙungiyoyin kwadago suka ba gwamnati domin kammala tattaunawar ya cika.

Asali: Legit.ng

People are also reading