Home Back

Gwamna Sani ya kaddamar da shirin bayar da rancen Naira miliyan 500 ga ma’aikatan jihar

premiumtimesng.com 2024/5/17
Gwamna Sani ya kaddamar da shirin bayar da rancen Naira miliyan 500 ga ma’aikatan jihar

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya kaddamar da shirin bayar da rance na Naira miliyan 500 ga ma’aikatan gwamnati.

Sani ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Kaduna yayin bikin ranar Mayu na 2024.

Ya kuma jaddada aniyar sa na ba da fifiko ga jin dadin ma’aikata da kuma samar musu da kayan aiki yadda ya kamata.

Sani ya jaddada muhimmancin hada karfi da karfe domin samun nasarar shirin gwamnatinsa na kawo cigaba a karkara da kananan hukumomin mu.

“Taken gwamnatina ita ce,’Jama’a ne farko, daga nan komai ya biyo baya, sai na gwangwaje talakawa da mutanen Karkara duma shu shaida”

Gwamnan ya kuma bayyana ci gaba da tuntubar juna da kungiyoyin kwadago a matakin tarayya da na jihohi domin tattaunawa akan karin albashin ma’aikatan jihar da kananan hukumomi.

Daga nan sai ya raba wa wasu daga cikin ma’aikatan cek din kuɗi ya yin da aka rika yi masa kirari don murna da salon mulkin sa a Kaduna.

People are also reading