Home Back

HARƘALLAR ƊAUKAR KURATAN ‘YAN SANDA: Gamayyar Ƙungiyoyin Ma’aikatan Hukumar ‘Yan Sanda na so Tinubu ya kori Sufeto Janar Egbetokun

premiumtimesng.com 2024/7/3
Ba mu ce za mu kori mata ‘yan sanda masu auren farar hula da ke zaune a bariki ba -Sufeto Janar

Gamayyar ƙungiyoyin Ma’aikatan Hukumar ‘Yan Sanda ta Ƙasa (PSC) ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta korar Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun.

Sun nemi a tsige shi bisa zargin rashin iya aiki da laifin ƙoƙarin haddasa rashin zaman lafiya a Najeriya.

Ma’aikatan sun kuma nemi Kakakin Yaɗa Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya nemi afuwar Hukumar PSC dangane da watsa ƙarya da sharri, inda ya saki wata sanarwa ga manema labarai, dangane da badaƙalar ɗaukar kuratan ‘yan sanda.

Kungiyar ta yi wannan kira ne ranar yau Laraba, yayin wani taron manema labarai a Abuja.

“Mun fara wannan taron manema labarai da yin kira ga Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gaggauta korar Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun.

“Damuwar mu ta taso ne ganin yadda a matsayin da na babban ma’aikatacin gwamnati, zai kitsa wa jama’a ƙarya da ƙaƙalo sharri wanda zai iya haddasa ruɗani a ƙasar nan.”

Shugaban Haɗaɗɗiyar Kungiyar, Adoji Adoyi ne ya bayyana haka.

Wannan haɗaddiyar ƙungiya dai ta ƙunshi Manyan Ma’aikatan Hukumar (ASCSN) (da NCSU).

Kiran ya biyo bayan Hedikwatar Rundunar ta ƙi karɓar kuratan ‘yan sandan da Hukumar PSC ta ɗauka.

People are also reading