Home Back

Taron Ministoci Karo Na 10 Na Dandalin Tattauna Hadin Gwiwar Kasar Sin Da Kasashen Larabawa Ya Zartas Da Wasu Takardun Sakamako

leadership.ng 2024/7/3
Taron Ministoci Karo Na 10 Na Dandalin Tattauna Hadin Gwiwar Kasar Sin Da Kasashen Larabawa Ya Zartas Da Wasu Takardun Sakamako

Yau Alhamis 30 ga wata, an yi nasarar gudanar da taron ministoci karo na 10, na dandalin tattauna hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin, inda aka cimma nasarori masu yawa.

Taron ya zartas da wasu takardu guda uku, ciki har da sanarwar Beijing, da shirin aiwatar da ayyukan dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa daga shekarar 2024 zuwa 2026, da sanarwar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa kan batun Palasdinu.

Har ila yau, a yayin taron, kasar Sin ta rattaba hannu kan wasu takardun hadin gwiwa tsakanin bangarori biyu, tare da kasashe masu halartar taron, da sakatariyar kawancen kasashen Larabawa. (Bilkisu Xin)

People are also reading