Home Back

An halaka mutum 2600, wasu 489,245 na zaman gudun hijira cikin shekara ɗaya a Jihar Benuwai – AI

premiumtimesng.com 4 days ago
DURƘUSA WA WADA BA GAJIYAWA BA NE: Gwamna ya roƙi ‘yan bindiga su saki Shugaban  Ƙaramar Hukuma da suka kama

Ƙungiyar ‘Amnesty International’ ta tabbatar da ƙididdiga cewa an kashe ƙimanin mutum 2,600 cikin shekara ɗaya a faɗace-faɗace daban-daban a Jihar Benuwai.

Ƙungiyar ta Jinƙai ta Duniya ta ce yawancin waɗanda aka kashe ɗin mata ne da ƙananan yara a yankunan karkara guda 50, a hare-hare daban-daban tsakanin watan Fabrairu 2023 zuwa Fabrairu 2024.

Daraktar Tsare-tsare ta AI, Barbara Magaji ce ta bayyana haka lokacin da take taro da manema labarai, ranar Laraba a Makurɗi, Babban Birnin Jihar Benuwai.

Barbara ta ce ƙananan hukumomi 18 daga cikin 23 da Jihar Benuwai ke da su duk su na fama da yawan kai masu hare-hare daga masu ɗauke da muggan makamai.

“Waɗannan mahara su na kawo cikar da wadatar abinci da kuma ga rayuwar al’umma, saboda mafi yawan kashe-kashen manoma ya fi shafa, waɗanda ake tarwatsawa daga gidajen su kuma noma ya gagare su.

“Daga watan Maris akwai masu zaman gudun hijira a sansanoni daban-daban za su kai su 489,245,” inji Barbara.

Daga nan ta ruwaito ƙididdigar da Ma’aikatar Ilmi da Hukumar Koyarwa ta Jihar Benuwai suka fitar cewa an lalata aƙalla makarantu 55 sanadiyyar hare-haren ‘yan bindiga, lamarin da ya tilasta rufe makarantun.

Ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su gaggauta kawo ƙarshen wannan munmunan kashe-kashe a Benuwai domin a kare rayukan jama’a.

People are also reading