Back to the last page

Yan bindiga sun bude wuta kan masallata a arewaci da kudancin Najeriya

dw.com 13 minutes ago

An kai hare-hare kan masallatai a jihohin Delta da Katsina da ke Najeriya a ranar Asabar da ta gabata, an yi garkuwa da mutane da dama da kuma halaka limami guda.

Nigeria Kankara | Angriff auf Schule | Entführte Schulkinder

A jihar Delta da ke Kudancin Najeriya, wasu 'yan bindiga ne suka bude wuta kan masallata inda daga bisani suka yi garkuwa da mutum uku, mutum akalla goma sha daya. Alhaji Badamasi Saleh, shugaban 'yan arewa mazauna jihar Edo ya mana karin bayani...

Hakazalika a Najeriya, a ranar Asabar da ta gabata, wasu 'yan bindiga sun bude wuta a wani masallaci, a daidai lokacin da jama'a ke sallar Isha'i a yankin Funtuwa da ke jihar Katsina, inda suka kashe limamin masallacin tare da yin garkuwa da masallata akalla goma sha takwas. 
 

Back to the last page