Gwamnati Za Ta Yi Gwanjon Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki Guda 5, Abubuwa Sun Lalace
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja -A jiya ne gwamnatin tarayya ta sha alwashin sayar da kamfanonin rarraba wutar lantarki guda biyar (DisCos) yayin da ake ci gaba da rashin wuta a kasar.
Gwamnatin tarayya ta kuma soke kwangilar samar da mitoci ta Dala miliyan 200 da ta bayar tun a 2021 amma aka gaza aiwatarwa, jaridar The Nation ta ruwaito.
A baya ne bankuna da kamfanin kula da kaddarori (AMCON), suka karbi ragamar kula da wadannan DisCos din saboda gazawar hukumomin wajen biyan basussuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu ya ce bankuna da AMCON ba su da karfin fasahar tafiyar da kamfanonin rarraba wutar.
Adelabu ya kara da cewa ana sa ran kammala siyar da manyan kamfanonin samar da wutar lantarki a cikin watanni uku ga wadanda aka san suna da karfin kula da su.
Jaridar Premium Times ruwaito cewa masu zuba jari suna ke rike da kashi 60% na hannun jari a cikin kamfanonin yayin da gwamnatin tarayya ke rike da kashi 40%.
Ana ci gaba da samun matsalar wutar lantarki a yawancin jihohi tare inda kamfanonin DisCos ke alakanta hakan daga ƙarancin kason wutar daga tashar wutar ta ƙasa
Haka kuma sun alakanta rashin wutar da ƙarancin iskar gas ga kamfanoni masu samar da wutar (GenCos) a da da sauran dalilai.
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa bata gari sun lalata hasumiyoyin wutar lantarki a hanyar Jos.
A cewar TCN wannan ya jawo daukewar wuta a jihohin Adamawa, Gombe da Taraba, yayin da ya ce yanzu yana kokarin gyara wutar Gombe ta hanyar amfani da tashar lantarki ta Bauchi.
Asali: Legit.ng