Home Back

Mummunar Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Arewa, ’Yan Kasuwa Sun Tafka Asara

legit.ng 2024/5/9
  • Wata mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar jihar Kwara, inda 'yan kasuwa suka tafka asara mai yawa a gaban idanunsu
  • An ruwaito cewa akalla shaguna biyar ne suka kone kurmus yayin da har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba
  • Gobarar ta tashi a daren ranar Talata, ta yi ta ci har zuwa lokacin da 'yan kwana kwana na tarayya da na jiha suka kawo dauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kwara - Wata mummunar gobara da ta tashi a safiyar ranar Talata ta babbake shaguna da dama a babbar kasuwar Owode da ke Offa, jihar Kwara.

Gobara ta tashi a babbar kasuwar Offa, jihar Kwara.
Akalla shaguna biyar ne gobara ta babbake a kasuwar Offa da ke jihar Kwara. Hoto: @Fedfireng Asali: Facebook

'Yan kwana kwana sun kashe gobarar

Wani bidiyo da jaridar The Nation ta gani ya nuna yadda gobarar ta rika cinye shaguna yayin da 'yan kasuwa suka gaza kashe ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan wutar ta yi yawa. Ba na tsammani wutar lantarki ce ta haddasa ta. Watakila wasu ne ke yin girki wutar ta kama, domin ta yi yawa sosai."

- A cewar wani dan kasuwa da aka ji muryarsa a cikin bidiyon.

SaharaReporters ta ruwaito cewa cewa jami'an hukumar 'yan kwana kwana na tarayya da na jiha ne suka taru suka kashe wutar.

"Yan kasuwa sun tafka asara" - Majiya

Wata majiya ta shaida cewa akalla shaguna biyar ne gobarar ta lakume su.

Majiyar ta ce:

"Har yanzu hukumomi na kan tantance lamarin, amma dai a ganin ido na, shaguna biyar sun kone kurmus.
"Muna maganar duniyoyi na miliyoyin Naira ne aka yi asararsu a wannan gobarar, amma na san hukuma za ta fitar da bayani nan gaba."

Gobara a garuruwan jihar Kwara

Wannan gobarar na zuwa ne kasa da watanni takwas da aka samu tashin gobara a wani gida da ke cikin garin, wadda ta lalata dukiyar N6.5m.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa gobarar ta tashi misalin karfe 1:05 na dare a Kowope da ke yankin Olorunkuse, a Offa.

Haka zalika, a watan Disamba, akalla shaguna 14 ne suka babbake a garin Tanke da ke karamar hukumar Ilorin ta Kudu da ke Kwara.

Gobara ta tashi a kasuwar Kaduna

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar Panteka da ke jihar Kaduna.

An ruwaito cewa bangaren 'yan katako a kasuwar ne ya kama da wuta, lamarin da ya jawo aka yi asarar dukiya mai yawa.

Asali: Legit.ng

People are also reading