Home Back

TA KWAƁE WA GWAMNONI: Kotun koli ta tabbatar da cin gashin kan kananan hukumomi

premiumtimesng.com 2024/8/23
ZAMAN SHARI’AR JAYAYYA DA TINUBU: Kotu ta ce lauyoyi su daina ƙaƙale-ƙaƙale, mai hujja ya baje ta a faifai kawai

Kotun koli ta tabbatar da cin gashin kan kananan hukumomi 774 na Najeriya, kuɗaɗen su su shiga aljihun su darek ba tare da gwamnoni sun yi musu katsalandan ba.

A hukuncin da ta yanke a ranar Alhamis, kwamitin mutane bakwai na kotun ya amince da kararrakin da gwamnatin tarayya ta gabatar na karfafa ‘yancin kananan hukumomin kasar nan.

Ɗaya daga cikin mambobin kwamitin, Emmanuel Agim, wanda ya gabatar da hukuncin kotun, ya ce daga ranar Alhamis ya kamata kananan hukumomin kasar nan su karbi kason su kai tsaye daga hannun
Akanta Janar na Tarayya.

Sabon tsarin da Kotun Koli ta bayar ya baiwa Akanta-Janar na Tarayya damar ketare gwamnatocin Jihohi wajen rabon kudaden da gwamnatin tarayya ke rabawa kananan hukumomi duk wata wanda a baya sai ya bi ta hannun gwamnatocin jihohi tukunna.

Shekaru 20 kenan kananan hukumomi na yin bauta ga jihohi, sun zame bayin jihohi, sai abinda aka ba su, wanda ba ya wuce su iya biyan albashi kawai.

Gwamnoni ke zaɓen wanda suke so su kuma tsige wanda suke so. Babu aikin da karamar hukuma za ta iya yi sai abin da gwamnoni suka ce shi za a yi.

Bisa ga hukuncin kotun koli, daga wannan wata ta Yuli, kowacce karamar hukuma za ta rika amsar kuɗin ta kai tsaye ne daga asusun gwamnatin tarayya, ba tare da wani gwamna ya yi mata tsalandan ba.

A baya akan samu ayyukan cigaba matuka karkashin kananan hukumomi, amma tun bayan sauya fasalin samun kudaden su lamarin ya canja. Iya ka su je aiki, idan wata ya ƙare su karɓi albashi kowa ya kama gaban shi.

People are also reading