Home Back

Rashin Wadatar Kayan Aiki: Yadda Nijeriya Ta Kasa Dakatar Da Asarar Naira Tiriliyan 1.4 A Sashen Kiwon Lafiya

leadership.ng 2024/7/1
Rashin Wadatar Kayan Aiki: Yadda Nijeriya Ta Kasa Dakatar Da Asarar Naira Tiriliyan 1.4 A Sashen Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawuran da ta dauka na aiwatar da tsare-tsaren da za su kai ga farfado da bangaren kiwon lafiya, lamarin da ke bude wagegen hanyar kashe makudan kudade a bangarorin kiwon lafiya, kama daga gine-ginen asibitoci, kayan aiki, maguna, wanda ya janyo rashin samun kiwon lafiya mai inganci.

Dukkanin gwamnatocin baya da na yanzu sun himmatu wajen samar da kiwon lafiya cikin rahusa da sauki ga jama’a, amma alkarin har yanzu bai samu cimmawuwa ba.

LEADERSHIP ta labarto cewa gwamnatin tarayya ta sanya kiwon lafiya cikin muhimman bangarorin da take bai wa fifiko, amma tsawon shekaru babu wani abun a zo a gani da ta iya tabuka a bangaren.

A cewar gwamnatin, daga cikin manufarta na ganin an samar da kiwon lafiya mai inganci cikin rahusa, shi ne kawo mafita ga matsalolin kiwon lafiya, rungumar sabbin hanyoyin fasa, da kuma rage yawan kashe kudaden neman jinya zuwa kasashen ketare.

Sai dai har yanzu tsarin kiwon lafiya a asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu na fama da matsaloli ciki har da na rashin ci gaba da rashin wadatar kayan aiki. Asibitocin gwamnati ma sun fi fama da matsalar rashin kyawun kayan abinci, gine-ginen da suka dace, rashin maguna da karancin kwararru da kuma karancin kudaden gudanarwa.

Masu lura da lamuran sun ce wadannan matsalolin sun kasance dalilin da ke janyo rashin samun kiwon lafiya a kan lokaci.

Yankunan karkara na kan gaba wajen fama da rashin asibitoci da samun kiwon lafiya idan aka kwatanta da birane. Asibitoci masu zaman kansu ma sun fi na gwamnatoci wadatar kayan aiki, lamarin da ke sanya jama’a kashe makuden kudade wajen neman jinya a asibitocin kudi.

A cewar BPE, dala biliyan (Tiriliyan 1.4) ne ake rasawa duk shekara wajen jinya ga dubban ‘yan Nijeriya da ke zuwa kasashen waje domin neman kiwon lafiya mai inganci da nagarta.

Bangaren kiwon lafiya a Nijeriya na fuskantar gibin kudade, wanda aka kiyasce cewa biliyoyin daloli ne ke salwanta a duk shekara.

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ba da shawarar a kara ware kaso 15 na kasafin kudin kowace kasa ga sashin kiwon lafiya, sai dai kasafin Nijeriya na gaza cika wannan shawarar. A shekarun baya, Nijeriya tana ware kaso 4-5 ne duk shekara ga bangaren kiwon lafiya, lamarin da ke barin wagegen gibi na kudade.

Sashin kiwon lafiya a jihohi na cikin halin ha-ula’i, asibitoci da dama ba su da wadatar kayan aiki da na kwararru. A wasu asibitoci da dama, hatta wutar lantarki, ruwa da sauran muhimman abubuwa ba su samu balle a yi maganar ingancinsu, lamarin da ke janyo babban matsala wajen samar da kiwon lafiya mai nagarta.

Bugu da kari, akwai matsalar ma’aikatan kiwon lafiya, daktoci, nas-nas, kwararru, inda wasu suka zabi su tafi kasashen waje domin yin aiki a maimakon yi a Nijeriya sakamakon matsalolin da bangaren kiwon lafiya ke fuskanta ciki har da rashin biyan kudin da ya dace da sauransu.

Lamarin na kara janyo karancin ma’aikatan kiwon lafiya da ke janyo yawan mace-mace, karancin samun aminci da asibitocin gwamnati.

Nijeriya kasa ce da take kan gaba wajen yawaitar mace-macen yara jarirai da mata masu juna biyu, yawan kamuwa da cutuka da suka hada da maleriya, tarin fuka, cuta mai karya garkuwar jiki, cutar suka, yawan jini da sauran cutuka masu hatsari, kuma asibitoci na fuskantar manyan kalubale.

Wata daktar da ta nemi a sakaye sunanta da ke aiki da gwamnatin tarayya ta ce, “Rashin wadatar kudade na daga cikin manyan matsalolin da sashin kiwon lafiya ke fuskanta, wanda hakan ke janyo karancin ba da kiwon lafiya da samun sakamako mai inganci,” ta shaida.

A bisa rashin wadatar kayan aiki da kwararru a kasar nan, ‘yan Nijeriya da dama sukan yanke shawarar fita kasashen waje domin neman lafiya, lamarin da ake asarar makuden kudade, domin fita jinyar na lakume musu miliyoyin naira ga kowani majinyaci.

A kiyasin da aka yi, ‘yan Nijeriya na kashe dala biliyan 1.2 a kowace shekara wajen yawon neman lafiya a kasashen waje, domin neman jinya mai inganci a kasashe irin su India, Amurka, Ingila da sauransu.

Ma’aikatan kiwon lafiya da dama sun ce domin shawo kan gibin da ake da shi a bangaren kiwon lafiyan jihohi da na tarayya, akwai bukatar sake fasalin tsarin kiwon lafiya da ake tafiya a kai da kuma zuba makuden kudade a fannin.

Wani likita a Abuja, Dakta Idris Hameed, ya shaida cewa, “Akwai bukatar gwamnati ta kara kasafin kudin da take ware wa sashin kiwon lafiya, da tabbatar da cewa kudaden da aka ware an yi amfani da su bisa gaskiya kuma yadda ya dace.

“Bugu da kari, hadin kai da masu zaman kansu na da matukar muhimmanci ta yadda za a samu shawo kan gibin da ake da shi wajen samar da kiwon lafiya mai inganci.

“Akwai bukatar a kara horas da ma’aikatan kiwon lafiya, da daukan sabbi, ba da yanayin aiki mai inganci. Shawo kan irin wadannan matsalolin na bukatar hadin gwiwar kowa da kowa daga bangaren masu ruwa da tsai, ciki har da gwamnatici, masu zaman kansu na kasashen waje domin tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya na samun wadataccen kiwon lafiya kuma mai inganci,” ya shaida.

People are also reading