Ana Gyara Gini Ya Ruguzowa Bayin Allah a Abuja, Mutane Sun Samu Raunuka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An samu mummunan haɗari yayin da wani gini ya rufta kan mutane a birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa hadarin ya jikkata wasu mutane yayin da ginin ya zubo masu a yammacin jiya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa ginin ya ruso ne a lokacin da wasu mutane da ake tunanin suna aiki a wajen ke cikin zagayen ginin.
Sai dai hukumomi sun tabbatar da cewa mutane uku ne kawai suka samu raunuka yayin da ginin ya ruso.
Rahotanni sun yi nuni da cewa ginin ya ruso ne a yammacin jiya Litinin da misalin karfe 4:40 da dare, rahoton Channels Television.
Kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce babu wanda ya rasu.
Sai dai rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa akwai mutane uku da suka jikkata kuma an tafi da su asibiti domin samun kulawa.
Rundunar ta bayyana cewa sun yi sauri domin tafiya wurin a lokacin da suka samu kiran gaggawa kan haɗarin.
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja tace an fafata tsakanin jami'an tsaro da 'yan fashi a karamar hukumar Abaji.
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igweh, ya ce an yi nasarar kashe 'yan fashi biyu a yayin fafatawar.
Asali: Legit.ng