Home Back

Majalisar Ɗinkin Duniya ta damu ya yawaitar sansanin masu gudun hijira a Benuwai, Adamawa, Barno da Yobe

premiumtimesng.com 2024/6/16
IDP-camp
IDP-camp

Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna matuƙar damuwa dangane da ƙara samun yawaitar sansanin ‘yan gudun hijira a jihohin Adamawa, Benuwai, Yobe da kuma Barno.

Wakilin UNDP a Benuwai, Adewale Oke ne ya bayyana haka, ranar Alhamis, lokacin da ya ke gabatar da jawabi taron neman hanyoyin shawo kan ƙalubalen yawaitar masu gudun hijira a Benuwai.

Ma’aikatar Agaji da Jinƙai ce ta shirya taron na kwana ɗaya tare da ƙungiyoyi daban-daban, cikin har da ‘yan jarida da mazauna sansanonin masu gudun hijira.

Oke ya ce kowace shekara tun daga ‘yan shekarun baya zuwa yau, ana ci gaba da samun ƙarin yawaitar adadin masu gudun hijira a sansanonin gudun hijira daban-daban.

Ya ce yawancin su mata ne da matasa da kuma dandazon marasa galihu da ƙananan yara.

Sai dai kuma ya yi alƙawarin cewa dukkan cibiyoyin da ke ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya, za su bijiro da hanyoyin da za a bi domin shawo kan wannan gagarimar matsala, musamman a Jihar Benuwai.

“Duk shekara sai ƙarin yawan masu gudun hijira a Benuwai, Barno, Adamawa da Yobe, sun nunnunka. Kuma yawancin su duk marasa galihu ne a cikin sansanin.

“Wannan lamari ya kawo cikas ga yara masu zuwa makaranta, mutanen da keman abin da zasu ciyar da iyalan su, sai kuma ga matan da ke ƙoƙarin samar da zaman lafiya a gidajen su.”

Ya ce shawo kan matsalar ba nauyin ɓangare ɗaya ba ne, tilas sai an haɗa ƙarfi da hannu.

Kwansitushin Agaji na Jihar Benuwai ya ce gwamnatin jihar na yin bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta maida masu gudun hijira zuwa garuruwa da gidajen su.

Aƙalla rahotanni sun tabbatar akwai masu gudun hijira fiye da miliyan 1 a sansanonin gudun hijira daban-daban a Jihar Benuwai.

Sun yi gudun hijira ne saboda yawaitar rikice-rikicen yankunan ƙabilu daban-daban.

People are also reading