Home Back

'Yan Najeriya Sun Taso Hadimin Tinubu a Gaba Kan Batun Yajin Aikin NLC, TUC

legit.ng 2024/7/2
  • Bayo Onanuga ya yi kakkausar suka kan yajin aikin sai baba ta gani da ƙungiyoyin ƙwadago suka shiga a faɗin ƙasar nan
  • Hadimin shugaban ƙasan ya koka da cewa matakin shiga yajin aikin zai cutar da mutanen da ƴan ƙwadagon suke iƙirarin suna karewa
  • Ya yi zargin cewa akwai siyasa cikin lamarin yajin aikin saboda kusan dukkanin shugabannin NLC, TUC suna goyon bayan jam'iyyar Labour Party ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hadimin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga, ya yi Allah wadai da yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka fara a faɗin ƙasar nan.

Mai taimakawa shugaban ƙasan kan harkokin yaɗa labarai da dabaru ya nuna takacinsa kan matakin da suka ɗauka na fara yajin aikin.

'Yan Najeriya sun caccaki hadimin Tinubu
'Yan Najeriya sun caccaki Bayo Onanuga Hoto: Bayo Onanuga Asali: UGC

Yajin aiki: Me hadimin Tinubu ya ce?

Bayo Onanuga ya nuna takaicin nasa ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, yayin da yake martani kan rufe filayen jiragen sama da katse wutar lantarki da ƴan ƙwadagon suka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onanuga ya bayyana cewa ƙungiyoyin ƙwadagon suna cutar da mutanen da suke iƙirarin cewa suna karewa.

Hadimin Shugaba Tinubun ya yi zargin cewa ƙungiyoyin ƙwadagon suna yin wasan siyasa ne da rayuwar mutanen Najeriya.

Ya bayyana cewa da yawa daga cikin mambobin ƙungiyoyin NLC da TUC ƴaƴan jam'iyyar Labour Party (LP) ne.

"Suna jin zafin gwamnatin Tinubu. Abin da yake a bayyane shi ne abin da suke iƙirarin suna fafutuka a kansa ba za a iya warware shi ta hanyar barazana ko ɓarna ba, gwamnatin tarayya ita kaɗai ba za ta iya warware shi ba."
"Shugabannin ƙwadagon dole sai sun sake dawowa kan teburin tattaunawa."

- Bayo Onanuga

Ƴan Najeriya sun caccaki hadimin Tinubu

@odubela81 ya rubuta:

"Shin N30,000 ne albashinka?"

@everestking1 ya rubuta

"Abin kunya ne a gareka ka riƙa haɗa abin da ke faruwa a Najeriya da siyasa. Bana tunanin cewa matarka tana gaya maka farashin kayayyaki a kasuwa."

@bruzieee ya rubutua:

"Shekara ɗaya bayan cire tallafin man fetur har yanzu ba a ƙara albashi ba. Amma ka ke rubuta haka?"

@plan_do_check ya rubuta:

"Oga Ade nawa ake biyanka N30,000? Ta shi daga nan"

An rufe majalisar tarayya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ma'aikatan majalisar tarayya (PASAN) ta shiga yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suke yi a faɗin ƙasar nan.

Shugabannin ƙungiyar sun rufe harabar majalisar tarayyar yayin da suka datse ruwa da wutar lantarkin da ke zuwa cikin majalisar.

Asali: Legit.ng

People are also reading