Home Back

Tiktok zai kalubalanci dokar shugaba Biden

dw.com 2024/5/18
Symbolbild TikTok USA
Hoto: Olivier Douliery/AFP

Shugaban kamfanin na sada zumunta da ake wallafa gajerun sakonnin bidiyo, Shou Zi Chew ya ce zai yi duk abun da ya kamata wajen kalubalantar sabuwar doka da ke barazanar haramta amfani da TikTok a Amurka. Kamfanin na TikTok ya ce zai dauki matakin shari'a wajen yin fito na fito da wannan doka da ke kokarin take 'yancin fadin albarkacin baki. Tun dai a lokacin da majalisar wakilan kasar ta amince da dokar kafin ta gabatar da ita ga shugaban kasar, shugaban kamfanin ya sha alwashin yin tsayin daka domin ganin hakan bai tabbata ba.

Shugaban kamfanin TikTok kenan Shou Zi Chew ya ce, mun ji majalisar Amurka ta mika kudurin dokar da ya samu sa hannu shugaban kasar da nufin haramta amfani da TikTok a Amurkar. Wannan na nufin mutane fiye da miliyan 170 za su daina amfani da wannan kafa wajen sada zumunta. Babu tantama wannan haramci kan TikTok haramci ne kanku da muryoyinku. 'Yan siyasa ka iya fadin hakan amma kar su rude ku. TikoTok ya bada kafa ga Amurkawa domin a gansu a kuma ji su shi ya sa ma mutane da dama suka sanya manhajar cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Muna da karfin gwiwa kuma za mu yaki 'yancinmu a gaban kotu."

Dokar dai da shugaba Biden ya sanya wa hannu za ta bai wa TikTok wa'adin watanni tara ya sayar da kamfani domin ya tashi daga mallakin kasar Chaina, kuma fadar gwamnati ta White na iya kara wa'adin kawai da kwana casa'in. 'Yan Majalisar Amurkar dai na ganin Manhajar ta TikTok barazana ce ga tsaron kasar inda suke ganin bayanan masu amfani shafin ka iya fada wa hannun gwamnatin Chaina. Sai dai sakatariyar yada labarai ta fadar White House Karine Jean-Pierre na cewa

'Yan majalisa dai sun baje komai a fai-fai. Wannan ba batu ne na tursasa haramta manhajar ba ce, magana ce ta siyar wa da kuma tsaron kasar. Wannan ba damuwa ce ta Amirkawan da ke amfani da manhajar ba, damuwa ce ta juya akalar Tiktok kuma a bayyana yake karara abun da 'yan majalisa suka gabatar muka goyi baya. Muna son mu ganin sauyin wadanda suka mallaki manhajar ce. Abun da wannan sabuwar doka take nufi kenan."

Ko a baya gwamnatin tsohon shugaban kasar Donald Trump ta yi yunkurin haramta amfani da manhajar a shekarar 2020. A yanzu haka dai ana ganin samun mai sayan kamfanin na TikTok ba zai zamo da sauki ba musamman da zai mallaki guda daga cikin manhaja mafi shahara a duniya. Ba lalle ne a samu wanda zai mallaki kamfanin cikin sauri ba. Idan har kamfani na TikTok bai aiwatar da abun da sabuwar dokar ta tanada ba zai fuskanci janye shi daga manhajar Apple da kuma Google App store a fadin Amirka.

People are also reading