Home Back

DAMBARWAR SARAUTAR KANO: Ganduje ne ya shiga tsakani na da Aminu Ado – Sarki Muhammadu Sanusi II

premiumtimesng.com 2024/6/26
Ban yi kira da a tsige ko Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC ba – Gwamna Alia

Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ne ya ƙulla dukkan ƙaƙudubar rikicin sarautar Kano da ke faruwa a yanzu.

Cikin wata tattaunawar da ya yi da jaridar The Sun, wadda jaridu da dama suka buga a yau Asabar, Sarki Sanusi II ya ce waɗanda suka ci moriyar cire shin da aka yi shekaru huɗu da suka shuɗe, su na jin haushin abin ne saboda cirewar su ma ta shafe su a yanzu.

Duk da dai bai ambaci sunan Aminu Ado ba, to tabbas dai da shi yake.

“Wato abin da muke fuskanta yanzu lamari ne wanda haka kawai wani ya zo ya raba mu. To kuma a gaskiya irin wannan idan ta faru, sai a yi wa wasu mutane alfarma. Amma ba su nemi a ba su sarautar ba ma, amma aka ɗauka aka ba su tsawon shekaru huɗu.

“To yanzu kuma sarautar ta suɓuce masu. Matsalar a nan ba abin da ya faru yanzu ne silar wannan batarnaƙa ba.

“Abin da ya faru a baya shi ne ya haddasa wannan jayayyar. Lamarin kuwa ya faru ne shekaru huɗu baya. Domin da a ce hakan ba ta faru ba a wancan lokacin, to da ba mu kawo cikin wannan ja-in-ja ba. Tushen mu ɗaya (da Aminu Bayero). Haka kawai wani ya zo ya farraka kawunan mu. Ko a cikin iyalan ma ya ɗauki masarauta ɗaya ya bai wa ɗan wani ɗan ɗaya ɗakin.

“To yanzu kuma waɗanda aka ƙwace sarauta daga hannun su, bayan sun ɗanɗana tsawon shekaru huɗu, sai abin ya zame matsala kuma.

“Lokacin da Ganduje ya yi niyyar ƙirƙiro masarautu, bai samu wata saɗara ko ɗaya a Kundin Dokokin Jihar domin ya yi wa dokar kwaskwarima.

“Sai ya fara da yi wa Dokar Masarautar Kano kwaskwarima, ita da ɗaya dokar, wadda wata kotu ta hana shi aikwata.

“Haka kawai sai Ganduje ya ƙirƙiro wata doka, ya samar da masarautun da ba su a Kano.

“Ya kashe Masarautar Kano ya maida ta mai ƙananan hukumomi takwas kaɗai, abin da babu shi a tarihin Kano sama da shekara dubu ɗaya. Haka Bichi, Rano da Gaya duk ba su a shekaru dubu ɗaya.

“To waɗannan masarautu sun yi mulki na tsawon shekaru huɗu, sai wani gwamna ya hau ya ce zai soke wannan karan-tsaye da aka yi wa masarautar Kano. Ya ce a koma yadda ake tun shekaru dubu ɗaya da suka shuɗe.

“To abin da ya faru kenan. Ba wani ne aka ƙullata ko aka bijiro da ci masa mutunci ba. To amma tabbas waɗanda wannan tsigewa a yanzu ta shafa, za su yi haushi. Mun kuma fahimci haka. Amma ba za mu bari masarautun su tafi a daddatse ba, don kada wasu su ce idan an haɗe su sun cutu.

“Saboda haka ɗin da aka yi, don amfanar mu al’ummar Jihar Kano ne. Ni ɗin nan Allah ne ya san shin zan yi tsawoncin rai a kan mulki ko ba zan yi ba. Allah zai iya karɓar rai na gobe.”

People are also reading