Home Back

Masarautar Argungu Da Al’adunta (3) Bikin Kamun Kifi

leadership.ng 2024/7/6
Masarautar Argungu Da Al’adunta (3)  Bikin Kamun Kifi

Masu karatu, mun dan yi waiwaye kadan daga karshen tarihin da muka kawo a makon jiya domin muhimmancin Bikin Kamun Kifi na Argungu da kuma sada tarihin da ragowarsa wanda za mu kammala a wannan makon.

Idan ba a manta ba, mun bayyana cewa: Bikin Kifi na Argungu na shekara-shekara yana daga cikin manyan al’adun gargajiya a arewacin Nijeriya. Bikin na da dadadden tarihi. An fara shi ne lokacin da mai alfarma Sarkin Musulmi, Hassan Dan Mu’azu, ya ziyarci Masarautar Argungu a shekarar 1934, kuma an gudanar da shi ne don nuna karfin Kabawa da Sarki Muhammed Sama. Har zuwa shekarun 1960 bikin ya kasance nagarin kawai, amma a shekarar 1972 ya samu halartar Shugaban kasar Nijeriya, Janar Yakubu Gowon da takwaransa na Nijar, Hamani Diori. Saboda dalilai na siyasa, daga bisani bikin ya rasa goyon baya kuma babu wani da aka shirya daga shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2004. Bikin yanzu ya sake farfadowa kuma ya zama babban wurin jan hankalin ‘yan yawon bude ido.

Zuwa shekara ta 2009, bikin al’adu na Argungu na Duniya inda yake hadawa da wata babbar hawan durbar tare da dawakai 500 da mahayansu, da rakuma 120 da mahayansu, wadanda ke dauke da tutar masarautar Argungu tare da mahalarta daga sauran kabilu da yawa.

Babban kifin da aka kama ya kai nauyin kilogiuram 55, kuma an bayar da kyaututtuka a wannan kamun kifin saboda Shugaba Umaru Musa Yar’adua ya halarta, da matarsa, gwamnoni shida da sarakunan gargajiya da yawa. Bikin na shekarar 2009 ya kuma hada da wasannin ruwa, gasar harbi da kibiya da taron gangamin mota, wasan kwaikwayo da kungiyoyin raye-raye suka yi daga kasashen Nijar, Mali, Chadi da Benin, wasan kokawa da dambe, da kuma baje kolin kayan gona. Mahimmancin bikin ga tattalin arziki ya sa gwamnati ta adana wasu kayan tarihi da yawa da aka nuna a lokacin.

Shirin ban ruwa

An kuma yi tunanin gudanar da aikin madatsar ruwa ta Zauro a cikin shekara ta 1969 sai kuma an dade da samun jinkiri, har sai da aka kai shekara ta 2009. Aikin an kiyasta cewa zai yi iya samar da ban ruwa ga kadadar noma mai girman hekta 10,572 a cikin kogin Rima tsakanin Argungu da Birnin Kebbi. Amfanin gonar da za a fi amfana da su sun hada da shinkafa, masara, alkama, sha’ir da kayan lambu kamar su aya, albasa, tumatir, dankalin turawa da sauransu. Madatsar ruwan kuma za ta amfani masana’antar kamun kifi, mai mahimmanci a cikin jihar. Aikin ya kunshi fa’idodi masu yawa amma kuma an yi sabani game da abubuwan da zai iya haddasawa, tunda zai canza fasalin amfani da kasa, sanya wasu al’ummomin cikin yanayi na ambaliya. An taba jifar Sarkin Argungu a cikin wata zanga-zangar adawa da aikin.

Gidan kayan gargajiya

A watan Yunin shekara ta 2009 Masarautar Argungu ta gabatar da wata shawara ga Hukumar Kula da Gidajen Tarihi don adana kayan tarihi na Surame. Surame shi ne babban birni na Masarautar Kebbi, wanda Mohammadu Kanta Kotal ya kafa. Sanata Umaru Abubakar Argungu ya kuma nemi taimako don sanya Gidan Tarihi na Kanta cikin jerin abubuwan tarihi na Duniya. Ginin gidan kayan tarihin, kusa da babbar kasuwa, an gina shi ne a shekara ta 1831 wanda Yakubu Nabame ya gina kuma ya kasance a matsayin fadar Sarki har zuwa shekara ta 1942, lokacin da Turawan ingila suka gina sabuwar fadar mulki a lokacin mulkin Muhammed Sani.

A ranar 1 ga watan Yulin shekara ta 1958, aka bude shi a matsayin gidan kayan gargajiya, wanda ke ba da damar fahimtar tarihin rayuwar Jihar Kebbi. Gidan kayan tarihin yana da tarin makamai, wadanda suka hada da layu, mashi, takuba, itace, duwatsu, bakuna da kibiyoyi, bindigogin cikin gida har ma da ganguna da ake nunawa. Gidan kayan tarihin sanannen wuri ne da ake binne matattun sarakunan karamar hukumar.

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

People are also reading