Home Back

Gwamnan Gombe Ya Hori Shugabannin Kananan Hukumomi Su Yi Aiki Tukuru

leadership.ng 2024/5/18
gombe

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi kira ga sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomi 11 da mataimakansu da kansiloli 114 da su yi aiki tukuru domin ci gaban yankunansu, inda ya taya su murnar lashe zabe.

Ya kuma bukaci da su dauki zaben nasu a matsayin wani nauyi na yi wa jama’a hi-dima a irin wannan lokaci mai matukar muhimmanci.

Gwamnan a wata sanarwa da ya fitar dauke da sanya hannun hadiminsa, Ismaila Uba Misilli, biyo bayan sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Gom-be (GOSIEC) ta fitar, ya taya jam’iyyar APC mai mulki murnar samun gagarumar nasara a zaben. Ya bayyana jin dadinsa da yadda zaben ya gudana ba tare da tangarda ba.

Gwamnan ya kuma yaba wa hukumar zaben da jami’an tsaro bisa kokarin da suka yi wajen ganin an gudanar da zaben cikin sauki, wanda hakan ya taimaka wajen gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.
Ya kara da cewa, “Yayin da nake taya ku murna, ina kira a gareku duka, ka da ku ga nauyin da masu zabe suka dora muku a matsayin damar yin aiki kawai, ku yi iya kokarinku don sauke amanar da aka ba ku.”

Gwamna Yahaya wanda ya bayyana kananan hukumomi a matsayin matakai masu matukar muhimmanci, ya bukaci zababbun shugabannin kananan hukumomin su daura damarar samar da ingantaccen shugabanci wanda zai yi tasiri mai kyau ga rayuwar al’umma daga tushe bisa manufofi da tsare-tsaren jam’iyyar APC da gwamnati mai ci a jihar.

Idan dai ba a manta ba, hukumar zabe ta Jihar Gombe ta ayyana jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe dukkanin kujerun shugabannin kananan hukumomin ji-har 11 da kansilolinsu 114.

People are also reading