Home Back

Kotu ta kwace wasu kadarori na N11.1bn da ake zargin suna da alaƙa da Emefiele

legit.ng 2024/7/3

Lagos - Babbar kotun tarayya mai zama a jihar Legas ta kwace kadarorin N11.1bn na tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kotun ta bai wa gwamnatin tarayya umarnin wucin gadi ta karɓe kadarorin da suka kai darajar N11,140,000,000 na Emefiele, tsohon gwamnan CBN.

Godwin Emefiele.
Kotu ta kwace wasu kadarorin N11.1bn da ake zargin suna da alaƙa da Emefiele Hoto: Mr Godwin Emefiele Asali: Facebook

Mai shari'a Chukwujekwu Aneke ne ya bayar da wannan umarni a zaman shari'a na yau Laraba, 5 ga watan Yuni, 2024, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Alkalin ya amince da ƙwace manyan kadarorin biliyoyin Naira na Emefiele ne bayan lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo, ya shigar da buƙatar hakan.

Babban Lauyan ya shaidawa kotun cewa ana zargin Emefiele da amfani da kuɗin da ya sata wajen sayan manyan kadarori, kuma jawo wasu ya sa su wakilce shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading