Home Back

Rasha ta musanta zargin shirin mamaye Kharkiv

dw.com 2024/6/18
Shugaban kasar Rasha, Vladmir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladmir Putin

A lokacin da yake zantawa da kafar yada labaran Rasha, Shugaba Vladmir Putin ya ce Moscwo ta kai hari Kharkhiv ne domin rama harin da aka kai yankinta na Belgorod wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama.

A baya-bayan nan dai, Rashar ta zafafa kai hare-hare a yankin na Kharkiv inda take luguden wuta daga yankin Belgorod.

A gefe guda kuwa, Kungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta dakatar da wasu kafafen yada labaran Rasha guda hudu a kasashe 27 mambobin kungiyar, saboda zargin da take musu na yada manufa a kan mamayar da aka kaddamar a Ukraine.

People are also reading