Jerin Gwamnoni 23 da Suka Sauya Sheka Yayin da Suke Kan Mulki Daga 1999 Zuwa Yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Sauya sheka ba bakon abu ba ne a siyasar duniya, ba a bar Najeriya a baya wajen canza gida a kan mulki ko bayan rasa ofis ba.
Gwamnoni sama da 20 sun bar jam’iyyun da suka lashe zabe zuwa wata jam’iyya dabam.
Jaridar Leadership ta bibiyi tarihin siyasa tun daga shekarar 1999, ta bibiyi yadda gwamnoni suke ta tsalle daga jam’iyya zuwa jam’iyyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babu jihohin da gwamnoninta suka rika canza gida a shekarun nan kamar Sokoto, Imo da Abia, an samu haka sau bakwai a jihohin uku.
Jam’iyyun da wannan sauyin sheka ta shafa su ne: APGA, AD, ANPP, PPA, sai kuma APC.
Sauran jam’iyyun siyasar da aka fice daga cikinsu ko aka shigo su a cikin shekarun nan 24 su ne: PDP, AC, LP, ZLP da jam’iyyar DPP.
Legit Hausa tattaro gwamnonin da suka sauya-sheka a lokacin da suke mulki a Najeriya.
1. Attahiru Bafarawa
2. Aliyu Wamakko
3. Aminu Tambuwal
4. Orji Uzor Kalu
5. Theodore Orji
6. Boni Haruna
7. Murtala Nyako
8. Ikedi Ohakim
9. Rochas Okorocha
10. Mahmud Shinkafi
11. Bello Matawalle
12. Abdulfatah Ahmed
13. Isa Yuguda
14. Godwin Obaseki
15. Rabiu Kwankwaso
16. Rotimi Amaechi
17. Saminu Turaki
18. Muhammad Adamu Aleiro
19. David Umahi
20. Ben Ayade
21. Samuel Ortom
22. Babatunde Fashola
23. Olusegun Mimiko
Attahiru Dalhatu Bafarawa, Aliyu Magatakarda Wamakko da Aminu Waziri Tambuwal duk sun canza shekar siyasa a Sokoto.
Daga jerin za a fahimci cewa a Abia da Imo, sau biyu gwamnoninsu suna canza sheka bayan an zabe su a kan karagamr mulki.
Asali: Legit.ng