PDP ta Tsoma Baki kan Rikicin Ribas, Yayin da APC ke Neman a Sanya Dokar ta Baci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Rivers- Jam’iyyar PDP ta tsoma baki cikin rikicin siyasa da ke daukar sabon salo a jihar Ribas, inda ta gargadi shugabannin kananan hukumomi da wa’adinsu ya zo karshe su guji tayar da tarzoma.
Sakataren yada labaran jam’iyyar ta kasa, Mista Debo Ologunagba ne ya bayar da shawarar a sanarwar da ya fitar ranar Laraba a babban birnin tarayya Abuja.
A wani labarin da Vanguard News ta wallafa, Ologunagba ya kara da cewa tabbas wa’adin shugabancin kananan hukumomi na shekaru uku ya zo karshe kamar yadda doka ta tanada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’iyyar PDP ta nemi al’ummar jihar Ribas da kada su dauki dumi yayin da rikicin siyasar jihar ke kara kamari bayan gwamnati ta tabbatar da zuwan wa’adin shugabannin kananan hukumomi ya zo karshe.
Nigerian Tribune ta wallafa cewa jam’iyyar ta bayar da shawarar ne a yau, inda ta kuma shaida kara wa’adin sayar da takardar neman tsayawa takara a yayin babban taron da da zai gudana a 2024.
Tun da farko jam’iyyar ta sanya 17 Yuni 2024 da cewa ita ce ranar da za a rufe sayar da takardar, amma yanzu an kara wa’adin zuwa Juma’a Yuni 28, 2024.
A baya mun kawo labarin cewa gwamnatin jihar Ribas ta yi watsi da rigingimun siyasar jihar sannan ta rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomi 23 a jihar bayan wa’adin tsofaffin ya zo karshe.
Gwamna Siminalayi Fubara ne ya rantsar da shugabannin a fadar gidan gwamnati dake babban birnin jihar a Fatakwal cikin tsauraran matakan tsaro domin gudun rikici.
Asali: Legit.ng