Home Back

Senegal:Bassirou Diomaye zai karbi mulki daga hannun Sall

dw.com 2024/5/11
Hoto: SEYLLOU/AFP

A Talatar nan za a rantsar da sabon shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye, wanda zai karbi mulki daga hannun shugaba mai barin gado Macky Sall, bayan samun nasarar lashe zaben da aka gudanar a kasar.

Daga cikin mahalarta taron bikin a birnin Dakar, akwai shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammcin Afirka ECOWAS, kuma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da sauran shugabannin kasashen Afirka.

Mr Faye ya alkawarta yin iya kokarinsa wajen ganin an dawo da kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar cikin ECOWAS, wadanda aka dakatar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashen.

People are also reading