Rikicin PDP Ya Dau Zafi Yayin da Aka Kori Tsohon Dan Majalisa Ana Dab da Zaben Gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Jam’iyyar PDP a ƙaramar hukumar Oredo a jihar Edo ta ce ta kori Honorabul Omorogbe Ogbeide-Ihama daga jam’iyyar.
Ogbeide-Ihama tare da Philip Shaibu, tsohon mataimakin gwamnan jihar, a makon da ya gabata sun bayar da gudummawar sakatariyar yaƙin neman zaɓensu na gwamna ga jam’iyyar APC reshen jihar.
An kori tsohon ɗan majalisar wanda ya wakilci mazaɓar tarayya ta Oredo a majalisar wakilai bisa zarginsa da cin dunduniyar jam'iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban jam’iyyar PDP na mazaɓa ta 2, Lawrence Aguebor, ya bayyana korarsa daga jam’iyyar.
Ya ce an ɗauki matakin korar tsohon ɗan majalisar ne a wani gagarumin taro da mambobi da shugabannin jam'iyyar na mazaɓar suka yi.
A cewarsa, tun da farko an dakatar da shi na tsawon kwanaki 30 bayan haka kuma aka kafa kwamitin ladabtarwa.
Ya bayyana cewa kwamitin ya rubuta masa wasiku kuma ya kira shi a waya ya zo a zauna har sau biyar, amma Ogbeide Ihama Omoregie ya kasa bayyana a gabansu.
Lawrence Aguebor ya kuma buƙaci jama'a da kada su ƙara wata hulɗa wacce ta shafi jam'iyyar PDP da Omorogbe Ogeide-Ihama.
Asali: Legit.ng