Home Back

Sanusi vs Aminu Ado: Kotu Ta Dauki Mataki Kan Dambarwar Sarautar Kano

legit.ng 3 days ago

Babbar Kotun jihar Kano ta dage ci gaba da sauraron shari'ar da ake yi kan rigimar sarautar jihar zuwa ranar Alhamis

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar Kotun jihar Kano da ke sauraron korafi kan rigimar sarautar jihar ta dauki mataki a yau Talata 2 ga watan Yulin 2024.

Kotun ta dage ci gaba da sauraron shari'ar sarautar har zuwa ranar Alhamis 4 ga watan Yulin 2024.

Kwamishinan shari'a a jihar Kano da Majalisar jihar da kakakinta su suka shigar da korafi a gaban kotun, Daily Nigerian ta tattaro.

Masu korafin sun shigar da karar domin bukatar kotun ta dakatar da Aminu Ado da sauran sarakuna hudu game da ci gaba da kiran kansu a matsayin sarakuna.

Lauyan masu kara Ibrahim Isah-Wangida shi ya shigar da korafin a ranar 27 ga watan Mayun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading