Home Back

DALLA-DALLA: Hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke kan dambarwar masarautar Kano

premiumtimesng.com 2024/7/3
RUƊANIN TALLAFIN FETUR: Ina tausayin shugaban da za a yi 2023 – Khalifa Sanusi

A ranar Alhamis ce Mai Shari’a A. M Liman ya yanke hukuncin cewa kotu ta jingine naɗin Sarki Muhammadu Sanusi II kuma ta dakatar da Gwamnatin Jihar Kano rushe Masarautu biyar da ya yi, har sai abin da hukuncin ɗaukaka ƙarar da Gwamnatin Kano ya zartas.

Mai Shari’a ya ce ba daidai ba ne a ƙi bin umarnin kotu tun da farko.

1. Kotu ba soke naɗin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ta yi ba, jingine shi ta yi.

2. Kotu ba ta soke Dokar Majalisar Dokokin Kano ta 2024, jingine ta ta yi inda ta ce Gwamna ya yi azarɓaɓin amfani da dokar ya rushe masarautu kuma ya naɗa Sarki Muhammadu Sanusi II, ba tare da ya bi umarnin kotu na dakatar da naɗin da rushewar ba, tunda wani ya shigar da ƙara.

4. Kotu ta ce dokar da Majalisar Kano ta kafa na nan, amma aiki da dokar ce da Gwamnatin Kano ta yi aka jingine, domin har yanzu magana ta na kotu.

5. Kotu ta amshi roƙon gwamnatin Kano, inda ta ce kowa ya tsaya a matsayar sa, domin ta rigaya ta ɗaukaka ƙara. Kenan Aminu Ado ba zai koma kan mulki ba tukunna domin magana na kotu.

6. Wannan hukunci dai tamkar a bai wa Aminu da hannu hagu ne, sai kuma a karɓe da hannun dama.

6. Kotun ta amsa roƙon Aminu Babba Ɗan’Agundi na buƙatar kotu ta tabbatar da cewar dokar da ta rushe dokar masarautu ta 2019 an yi ta ba tare da girmama umarnin kotu ba. Don haka kotu ta juyar da matakin da Gwamnatin Jiha ta ɗauka.

8. Amma kotun ta matsa gaba ta tabbatar da buƙatar Majalisar Jihar Kano na a tsaya a matsayin da ake ciki yanzu. Don haka Sarki Sanusi shi ne Sarkin Kano tun da umarnin da ta bayar ba za a aiwatar da shi ba, har sai an saurari ra’ayin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara.

9. Haka kan kotun ta mayar da batun shari’ar zuwa wata kotun. Hakan yana nufin Alkali Liman ba shi zai ci gaba da sauraron wannan ƙarar ba, kuma ba shi ne zai yanke hukuncin ƙarshe ba, idan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke hukuncin cewa Babbar Kotun Tarayyar tana da hurumin sauraron ƙarar ko ba ta da shi.

10. Gwamnatin za ta iya bai wa Sarki Muhammadu Sanusi wata sabuwar takardar shaidar zama Sarki, idan ta janye ƙarar da ta ɗaukaka, domin kotu ba ta soke dokar Majalisar Dokokin Kano ba, jingine ta ta yi.

11. Wato dai kotu ta ce dokar rushe masarautu ta kafu, kuma masaurautun sun rusu, domin amma naɗin Sarki Muhammadu Sanusi na II ne aka jingine tukunna.

12. Idan masaurautun sun rusu, to Aminu ta tafi kenan, domin ba Sarkin Kano ba ne na ƙananan hukumomi 44, kamar yadda Sarki Muhammadu Sanusi II ya ke a yanzu. Sarki ne na ƙananan hukumomi 8 kaɗai. Hakan na nufin ba zai iya maye gurbin Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano baki ɗaya ba.

People are also reading