Rabi'u Pele, ɗan ƙwallon Kano da ke son buga wa Barca ko Arsenal wasa
Rabi'u Pele, ɗan ƙwallon Kano da ke son buga wa Barca ko Arsenal wasa
Mintuna 18 da suka wuce
Rabi'u Abdullahi wanda aka fi sani da Rabi'u Pele a Tudun Wada United da ke birnin Kano, Najeriya, ya ce burinsa shi ne ya buga wa Barcelona ko kuma Arsenal wasa.
Ɗan wasan wanda ya buga wa tawagar Najeriya a gasar WAFU Cup ta Afirka ta yamma da ta gudana a Ghana, na kuma fatan shiga tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya - Super Eagles.