Home Back

CAN Ta Roki Musulmai Bayan Fasto Ya Farmaki Musulmi Kan Yanka Ragon Layya, Ta Dauki Mataki

legit.ng 2024/7/3
  • Wani Fasto a jihar Oyo ya ci zarafin wani Musulmi da matansa biyu saboda yanka rago kusa da cocinsa a ranar sallah
  • Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Iseyin da ke jihar inda Kungiyar CAN ta dauki mataki kan Faston
  • Daga bisani Kungiyar a yankin ta ziyarci shugabannin Musulmai domin ba su hakuri kan abin takaicin da ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Kungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) reshen jihar Oyo ta roki gafarar al'ummar Musulmai a jihar.

Kungiyar ta yi rokon ne bayan wani Fasto ya farmaki wani magidanci da matansa biyu kan yanka ragon layya.

Kungiyar CAN ta roki Musulmai bayan Fasto ya farmaki wani Musulmi a Oyo
Kungiyar CAN ta dauki mataki kan Fasto bayan hari kan Musulmi saboda yanka rago a Oyo. Asali: Original

Kungiyar CAN ta roki al'ummar Musulmi yafiya

Shugaban kungiyar a karamar hukumar Iseyin, Apostle Sunday Ogundairo ya ce sun dauki mataki kan Faston, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sunday ya ce sun ci gaba da ba shugabannin al'ummar Musulmi a yankin hakuri domin kwantar musu da hankali, Oyo Echo ta tabbatar.

Wannan na zuwa ne bayan Faston da jama'ar cocinsa sun kai mummunan farmaki wani Musulmi mai suna Sulaimon AbdulAzeez da matansa biyu.

Hakan ya biyo bayan zargin AbdulAzeez ya yanka ragon layya yayin da yake kallon cocin wanda bai yiwa Faston dadi ba.

Lamarin ya faru ne a ranar sallah inda Faston ya kwaso mutumin da matansa har cikin coci inda suka yi musu jina-jina.

Kungiyar CAN ya dauki mataki kan Fasto

Kungiyar CAN a yankin ta dauki mataki kan Fasoton tare da unartansa da ya kaura da cocinsa daga wannan yankin.

Kungiyar ta ce ta sha sasanta Faston da iyalan mutumin wanda har sai da Sarkin Iseyin ya saka baki a rikicin nasu.

Musulmai sun hallaka wani matashi a Bauchi

Kun ji cewa Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta tabbatar da wani mummunan lamari da ya faru a kauyen Nasaru wanda ya yi sanadin mutuwar wani matashi.

A cewar sanarwar da kakakin rundunar a jihar, Ahmed Wakili wani matashi mai suna Yunusa Usman ne aka kashe saboda tallata sabon addini.

Ahmed Wakili ya bayyana cewa matashin ya fara yiwa mazauna kauyen da'awar addinin 'Fera Movement', lamarin da ya harzuka su, suka kashe shi.

Asali: Legit.ng

People are also reading