Home Back

Jihar Benuwai Ta Bankado Mutum 35 Masu Yi Wa Sirin Tattara Harajinta Zagon-Kasa

leadership.ng 2024/5/10
Jihar Benuwai Ta Bankado Mutum 35 Masu Yi Wa Sirin Tattara Harajinta Zagon-Kasa

Mukaddashin shugaban hukumar tattara haraji na Jihar Benuwe, Emmanuel Agena, ya sanar da cewa, sun samu nasarar cafke mutum 35 da ake zargin karbar kudin haraji daga al’umma ba bisa ka’ida ba, za kuma a tabbatar an hukunta su ba tare da bata lokaci ba. 

Ya kuma ce, hukumar tana hakoron tattara fiye da naira biliyan 16 a matsayin haraji a wannan shekarar ta 2024.

A ranar litinin ne shugaban hukumar ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai, ya ce a shekarar 2023 hukumar ta tattara fiye da naira biliyan 14, wannan kuma ya kasance fiye da yadda aka kiyasta a kasafin kudin shekarar.

Ya kuma ce, harkokin masu karbar haraji ba bisa ka’ida ba yana kawo cikas ga kokarin jjhar na tattara kudaden shiga, ya ce kuma  akwai wasu masu hannu da shu ni da ke goya musu baya a harkokin da suke yi na tattara kudade ba bisa ka’ida ba. A kan haka ya yi alkawarin kawo karshen masu wannan halayyar.

Ya kuma nuna bacin ransa a kan yadda wasu matasa suka yi wasoson kayan tallafin da wata babbar mota da ta taso daga Adamawa zuwa Anambara ta dauko a daidai garin Aliade da ke karamar hukumar Gwer ta gabas.

Ya ce, matasan sun kwace motar ne bayan sun yi wa direban dukan kawo wuka suka kuma kashe kayyan da aka kiyasata ya kai na naira 200,000, amma kuma tuni aka kama wadanda suka aikata wannan danyen aikin suna a hannun ‘yansanda za kuma a wuce da su wurin jami’an DSS don a gudanar da cikakken bincike tare da hukunta su.

“Za mu tabbatar da kawo karshen harkokin masu karbar haraji ba tare da doka ba, ya zuwa yanzu mun kama mutum 35 za kuma tabbata da ganin an hukunmta su ba tare da bata lokaci ba.

“Wannan baban kalubale ne, mun kafa kwamiti a karkashin wani daraka a hukumar don gangamin ganin an kawo karshen ayyukan wadanna bata garin.”

Shugaban hukumar ya kuma ce, a halihn yanzu sun shiya karbo fiye da naira biliyan 5.6 a matsayin kudin harajin kasa daga masu gidaje a fadin jihar.

People are also reading