Home Back

Meresca Ya Zama Sabon Kocin Chelsea, Ya Rattaba Hannu A Kwantiragin Shekara 5

leadership.ng 2024/7/3
Meresca Ya Zama Sabon Kocin Chelsea, Ya Rattaba Hannu A Kwantiragin Shekara 5

Enzo Maresca ya amince da rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea don zama sabon kocinta, wanda zai gaji Mauricio Pochettino.

Ana sa ran za a sanar da yarjejeniyar a hukumance kafin ƙarshen mako. Maresca, wanda ya jagoranci Leicester City komawa gasar Premier ta hanyar lashe gasar Championship, an zabe shi ne saboda zurfin iliminsa na tawagar Chelsea da kuma iya daidaitawa ƴan wasa da falsafar wasan ƙungiyar.

Darektocin wasanni na Chelsea, Paul Winstanley da Laurence Stewart, sun tattauna tare da Maresca bayan sun sami izini daga Leicester City. Rahotanni sun ce yarjejeniyar sakin dan ƙasar Italiyan daga Leicester ya kai fam miliyan 8 zuwa fam miliyan 10.

Sabon Kocin Chelsea, Enzo Maresca
Sabon Kocin Chelsea, Enzo Maresca
People are also reading