Home Back

TUWO NA MAI NA: APC ta lashe zaben Gombe kakaf, tun daga na Ciyamomi har Kansiloli

premiumtimesng.com 2024/5/18
TUWO NA MAI NA: APC ta lashe zaben Gombe kakaf, tun daga na Ciyamomi har Kansiloli

Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan zabukan shugabannin kananan hukumomi 11 da na kansiloli 114 da aka gudanar a jihar Gombe ranar Asabar.

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Gombe, Malam Sa’idu Awak wanda ya bayyana sakamakon zaben a Gombe, ya ce daga cikin jam’iyyu 19 da aka yi wa rajista a jihar, jam’iyyu biyar ne suka tsayar da ƴan takara a zaɓen.

Da yake jawabi kan sakamakon zaben shugaban jam’iyyar Accord Party a jihar Gombe, Mohammed Garba ya ce jam’iyyarsu ta shiga zaben ne domin tabbatar da kasancewarta a jihar.

Ya yi wa wadanda suka ci zabe fatan alheri

People are also reading