Home Back

Yanzu-yanzu: Hatsaniya Ta Kaure Tsakanin Sojoji Da Matasa A Gashuwa

leadership.ng 2024/5/13
Yanzu-yanzu: Hatsaniya Ta Kaure Tsakanin Sojoji Da Matasa A Gashuwa

Wata hatsaniya ta kaure tsakanin sojoji da matasa ‘yan Adai-daita sahu (Napep) a garin Gashuwa, shalkwatar karamar hukumar Bade a jihar Yobe, al’amarin da ya jawo raunuka a ranar Lahadi. 

LEADERSHIP ta gano cewa, hatsaniyar ta faro ne sakamakon wata rashin jituwar da ta kunno kai tsakanin bangarorin biyu.

Wata majiya a Babbar Asibitin Kwararru da ke garin Gashuwa, ta bayyana cewa, an kashe mutum daya, yayin da mutum 9 suka samu raunuka daban-daban.

Majiyar ta kara da cewa, “Abin da ya faru shi ne motar sojojin ce ta zo a guje, inda ta yi kicibis da motar Golf, a kokarin kaucewa ne soja daya ya fado, inda motar sojojin ta kade wata Keke Napep, wanda hakan ya jawo sojojin daukar mummunan matakin.

Gashuwa

“Wannan ya jawo matasan su ka harzuka tare da kulle babbar hanyar, ba shiga ba fita. Hakan ya jawo Shugaban Karamar hukumar Bade, Hon. Ibrahim Babagan Yurema, hadi da Maji-dadin Bade zuwa wajen domin baiwa matasan hakuri domin hana tashin-tashina.”

Duk kokarin jin ta bakin Rundunar ‘Yansandan jihar Yobe kan batun ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, lamarin ya cutura.

People are also reading