"Ba Ku Isa Ba": Gwamnoni Sun Shiga Uku, Majalisa Za Ta Yi Doka Kan Mafi Karancin Albashi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Majalisar Tarayya ta tabbatar da shirin gabatar da kudiri da zai tilasta gwamnoni biyan mafi karancin albashi.
Shugaban kwamitin hulda da jama'a na Majalisar, Sanata Yemi Adaramodu shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a 14 ga watan Yuni.
Adaramodu ya ce kudirin zai tilasta gwamnoni biyan mafi karancin albashin da zarar an tsayar da mafita, cewar Daily Trust.
Ya ce za a tabbatar da kudirin ya zama doka wanda za ta hukunta duka gwamanonin da suka ki bin tsarim mafi karancin albashi.
"Za mu samar da kudiri mai tsauri wanda Shugaba Tinubu zai sanyawa hannu domin bin tsari."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Idan muna maganar mafi karancin albashi, ba fada ba ne na iya Gwamnatin Tarayya da NLC saboda haka wasu ke ganin abin."
"Za mu samar da doka mai tsauri wanda jihohi ko ma'aikatu masu zaman kansu dole su bi dokar ko su fuskanci hukunci."
- Yemi Adaramodu
Kun ji cewa wasu ma'aikata a Najeriya sun bukaci gwamnonin jihohi su rage alawus dinsu domin biyan mafi karancin albashi.
Ma'aikatan sun bayyana haka yayin da kungiyar gwamnonin ta ce ba za ta iya biyan mafi karancin albashin N70,000 ba a halin da ake ciki.
Asali: Legit.ng