Home Back

El-Rufai Ya Shiga Sabuwar Matsala Yayin da Majalisar Kaduna Ta Kafa Kwamitin Bincike

legit.ng 2024/5/19

Jihar Kaduna - Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda aka tafiyar da jihar karkashin tsohon gwamna Nasir el-Rufai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

An dora wa kwamitin alhakin duba kudaden lamuni, tallafi, da yadda aka aiwatar da ayyuka daga 2015 zuwa 2023 lokacin da El-Rufai ke rike da jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.

Majalisar Kaduna za ta binciki gwamnatin El-Rufai
Kwamiti zai duba kudaden lamuni, tallafi, da yadda aka aiwatar da ayyuka daga 2015 zuwa 2023. Hoto: @elrufai Asali: Facebook

A ranar 30 ga Maris, Uba Sani, gwamnan Kaduna, ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin dala miliyan 587, da Naira biliyan 85, da kuma bashin kwangila 115 daga gwamnatin El-Rufai.

Da yake magana a yayin wani taro na jama'a, Sani ya kuma ce bai aro ko kobo ba a cikin watanni tara da suka gabata ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce, tulin bashin da gwamnatin El-Rufai ta bari yana cin kaso mai tsoka na kudaden da jihar ke samu daga rabon tarayya na wata-wata.

Karin bayani na zuwa...

Asali: Legit.ng

People are also reading