Home Back

Shin ko kun san halin da mata masu ɓoyayyen ciki ke shiga?

bbc.com 2024/10/6

Asalin hoton, Tawana Musvaburi

Baby River, being held by her mum Tawana - Tawana is also pointing a cuddly toy at the camera.
Bayanan hoto, Tawana ba ta san tana da juna biyu ba, sai dai yanzu ta haihu kuma har ƴarta mai suna Rivers ta kai shekara ɗaya

Haihuwa a shekara 21 ba ya cikin tsarin Tawana.

Ta ce ita mai son casu ce, inda take fita domin cashewa da ƙawayenta.

Haka ta ci gaba da yi har sai da ta tsinci kanta a asibiti bayan da ta yanke jiki ta faɗi.

Ba ta san mai ya sa hakan ya faru ba. A asibtin ne aka faɗa mata cewa za ta haihu cikin makonni huɗu masu zuwa.

"Na fara firgita," kamar yadda Tawana ta faɗa wa BBC.

Ta yi mamaki da jin labarin.

"Saboda wani yana faɗa maka, eh, nan da mako huɗu za ka haihu."

Bayan kwantar da ita a asibiti, likitoci sun buƙaci Tawana ta yi gwajin ciki.

Sai dai ta yi watsi da hakan - tana da tsarin kayyade iyali a hannunta kuma ba ta nuna alamun mai ɗauke da juna biyu ba.

Kuma lokacin da gwajin ya fita cewa ba ta da juna biyu, Tawana ta ƙara yarda cewa tana kan daidai.

Sai dai wata ma'aikaciyar jinya ta yi ƙoƙarin karfafa wa likitan cewa a ƙara yi mata gwaji, saboda tayi imanin cewa akwai yiwuwar Tawana na ɗauke da ciki.

Mahaifin Rivers, Emmanuel, ya ce lokacin da Tawana ta faɗa masa cewa ta kusa haihuwa, bai yarda da ita ba.

"Ba abin da hankali zai kama bane kwata-kwata," in ji shi.

Tawana and Emmanuel, with their baby, River after speaking to the BBC's Reliable Sauce podcast
Bayanan hoto, Tawana da Emmanuel, tare da ƴarsu River bayan tattaunawa da BBC

Haihuwa ba tare da nuna wasu alamu ba kamar amai ko kuma fitowar cikin shi ake kira ɓoyayyen ciki.

Ba a cika samun irin haka ba, sai dai Tawana ta ce likitoci sun faɗa mata cewa "an fi samun hak cikin al'ummomi bakake".

"An faɗamin cewa ana samun haka ne saboda kwankwason mu da kuma kasusuwan mu, jariri ba ya girma ta waje sai ta ciki," in ji ta.

"Don haka lokacin da zan haihu, babban damuwata shi ne kar jaririn ya juye."

Duk da cewa babu alkaluman mata masu ɓoyayyen ciki, Alison Leary, wata farfesa a sashen kiwon lafiya na Jami'ar South Bank da ke Landan, ta ce akwai alkaluma da yawa da suka nuna cewa bambanci a irin kulawar lafiya da ake bai wa mata da suka fito daga kabilu marasa rinjaye.

"Akwai bincike da yawa da ya nuna cewa mata, musamman bakake, ba sa samun kulawa idana aka zo ɓangaren ciki da kuma haihuwa," kamar yadda ta faɗa wa BBC Newsbeat.

Kuma tana ganin cewa akwai buƙatar a ƙara yin bincike kan batun da ya shafi mata masu ɓoyayyen ciki.

"Shi yasa ya zama batu mai muhimmanci duk da cewa ya shafi mutane kalilan ne kawai saboda idan ba ka samu kulawa tun da farko ba, akwai yiwuwar ka fuskanci sakamako mara kyau."

Makonni huɗu da kuma kwana huɗu bayan faɗa mata cewa za ta haihu, Tawana ta haifi ƴarta mai suna River.

Ta ce ta fuskanci kalubale bayan haihuwa, kuma ta ji kamar ta hau shafin TikTok don neman shawara kan yadda za ta kula da ƴarta ganin cewa tana da ƙananan shekaru.

Sai dai ta ce ba ta samu kowa ba, sai wata mata a Amurka wadda ita ma ta taɓa shiga irin yanayin.

"Na shiga tsananin damuwa saboda abun ya kasance kamar babu wanda zai ba ni shawara.

"Babu wanda yake magana kan wannan batu. Kamar, ya abun yake? Kuma ina ganin kamar na ga wani bidiyo, wanda aka kalla har sau ɗari na wata yarinya a Amurka da ke magana kan batun masu ɓoyayyen ciki.

"Kuma ya kasance kamar ita ce ta ba ni shawara."

Daga baya Tawana ta yanke shawarar bayyana abin da ta fuskanta kan kafofin sada zumunta, a cikin wani hoton bidiyo da ya samu makallata kusan 400,000.

Ta kuma fara yin wani shiri na intanet, inda take magana da sauran uwaye.

Tana jin cewa ta faɗi labarinta kuma tana fatan hakan zai sa uwaye matasa, waɗanda suka gano cewa suna da ciki dab da haihuwa, su samu ƙarin goyon baya.

A nata ra'ayin, tana son a kafa wata gidauniyar taimako.

"Babu wani taimako, don haka idan irin wannan lamari ya faru da kai, ya za ka yi?"

Mene ne ɓoyayyen ciki?

  • Kalma ce da ake amfani da ita idan mace ba ta san tana ɗauke da juna biyu ba - wasu mata na cewa ba su sani har sai sun kusa haihuwa.
  • Kusan haihuwa ɗaya cikin 2,500 sun kasance na matan da masu ɓoyayyen ciki ne
  • Alkaluman masu ɓoyayyen ciki da ke haihuwa a Birtaniya duk shekara ya kai 300
  • Ana danganta faruwar haka idan mace ta ƙasa ganin alamomin ciki
  • Ko da mata waɗanda ke samun ɗaukewar al'ada ko ma rashin ganinsa na fuskantar irin waɗannan alamomi
People are also reading