Home Back

Karin Albashi Ya Zama Karfen Kafa A Nijeriya

leadership.ng 2024/10/5
Batun Biyan Dubu ₦105 Mafi Ƙarancin Albashi Ƙanzon Kurege Ne – Fadar Shugaban Ƙasa

Tun bayan da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye tallafin fetur a lokacin da aka rantsar da shi nan take, kungiyoyin kwadago suka yi masa ca! tare da neman karin albashin ma’aikata domin a cewarsu, albashin da ake biya ba zai ishi ma’aikaci rayuwa ba sakamakon janye tallafin.

An shafe watanni ana kai-ruwa-rana a tsakanin gwamnati da ‘yan kwadago, har ta kai ga shiga yajin aiki karo na biyu a wannan makon duk dai a kan batun kara mafi karancin albashin. A farkon wannan makon, ‘yan kwadago sun jefa Nijeriya a cikin duhu sakamakon yajin aiki, domin nuna fusatarsu da “tayin wulakanci” da gwamnati ta yi musu a kan karin mafi karancin albashin.

Da farko ‘yan kwadago sun nemi gwamnati ta biya N615,000 a matsayin mafi karancin albashi, ita kuma gwamnati ta yi tayin N48,000. ‘Yan kwadagon suka sake ragewa ya koma N497, inda gwamnatin ta kara yin nata tayin zuwa N54,000, sannan ta kuma karawa zuwa N57,000. A tattaunawar karshe kafin shiga yajin aikin, ‘yan kwadago sun sake rage bukatarsu zuwa N494,000, ita kuma gwamnati ta kafe kai da fata a kan za ta biya N60,000, inda aka tashi barambaran tare da ayyana shiga yajin aiki ranar Litinin 3 ga Yuni, 2024.

Ganin yadda yajin aikin ya jefa kasa cikin wani mawuyacin hali, gwamnati ta samu nasarar rarrashin ‘yan kwadagon; su janye yajin aikin tare da dawowa teburin sulhu, inda ta nuna musu cewa; shugaban kasa yana da kudirin kara musu fiye da N60,000 da suka ki amincewa a baya. Wannan ya sa ‘yan kwadagon suka janye yajin aikin na tsawon mako guda, yayin da shugaban kasa kuma ya bai wa ministan kudi wa’adin kwana biyu ya fito da tsarin da za a biya karin mafi karancin albashin.

Ya Kamata A Sake Lale – Dr. Ahmed Adamu
Sai dai kuma, wasu masana tattalin arziki sun yi gargadin cewa; ya kamata a yi kaffa-kaffa da batun karin albashin ba tare da an samar da hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasa ba.

Masanin tattalin arziki, musamman bangaren man fetur, Dakta Ahmed Adamu ya bayyana cewa, ya kamata idan za a kara wa ma’aikata albashi; a duba a ga yadda za a kara yawan hanyoyin da za su habaka tattalin arziki, idan kuma ba haka ba; tsadar rayuwa za ta karuwa.
Kuma idan zai yiwu, a duba yiwuwar gyara a dokar da’ar ma’aikata da ta hana ma’aikaci yin kasuwanci kowane iri ne, in ban da aikin gona.

Ya yi wannan bayani ne a wani shirin gidan talabijin na Channelsa a ranar Laraba, inda ya ce tun da yanzu an samu sauyin zamani, za a iya gyara dokar ya zama ma’aikaci zai iya yin kasuwanci a hukumance, musamman ga hanyoyi nan na zamani a bangarorin fasahar sadarwa. Sai a rage yawan sa’o’in da ake zuwa aiki, domin bai wa ma’aikatan dama su rika gudanar da kasuwancinsu.

Haka zalika, ya shawarci gwamnati ta sake duba tsarin yadda take aiwatar da manufofinta na kudi, wanda yana daga cikin abubuwan da suka kara haddasa tsadar rayuwa.

Ya kara da cewa, idan farashin kaya ya yi tashin gwauron zabo, mutane ba su da kudin da za su saya. Don haka, a kawo matakai da tsare-tsare da za su bunkasa samar da kayayyaki da aikin gona da kuma sha’anin sufuri, wanda idan aka yi amfani da su; tabbas za su saukaka yanayin rayuwar da ake ciki.

Bayanan Mai Fashin Baki, Hon. Adamu Rabiu
Shi ma har ila yau, da yake tofa albarkacin bakinsa a shirinmu na Barka Da Hantsi Nijeriya da ake watsawa kai tsaye ta shafinmu na YouTube da Facebook (Leadershi Hausa), dan siyasa kuma mai fashin bakin al’amuran yau da kullum, Hon. Adamu Rabi’u, ya ce, “Kungiyar kwadago da gwamnati, Danjuma ne da Danjummai; domin kuwa ba talaka ne a gabansu ba, illa kadai wasa da rayukan ‘yan Nijeriya; dalili kuwa tun yaushe ake yin wannan batu guda daya, amma an kasa cimma matsaya?

“Tun farkon zangon wannan mulki na Tinubu aka fara wannan batu tare da kafa kwamiti na bangarori uku, suka bukaci a ba su Naira biliyan daya; a matsayin ladan aikin da kwamitin zai yi na duba nawa ne ya kamata a biya ma’aikacin gwamnatin tarayya hakkinsa na albashi.

“A nan ko kadan ba a yi batun ma’aikacin gwamnatin jiha ko na karamar hukuma ba, yadda al’amarin ya nuna kawai shi ne; gwamnatin tarayya ma’aikatanta ne kadai a gabanta ba sauran ma’aikatan Nijeriya baki-daya ba.”
Hon. Adamu ya kara da cewa, bai kamata a rika barin ma’aikatan jihohi da na kananan hukumomi a batun karin albashi a kasar nan ba, “Su ma bangaren ‘yan kwadago; hankalinsu ya fi karkata a kan ma’aikatan gwamnatin tarayya, saboda haka; baya ga ma’aikatan jihohi, kananan hukumomi da kuma kamfanoni masu zaman kansu, wadanda kuma ba sa yin aikin gaba daya ba fa, su kuma yaya za a yi da su?

“Sannan, wadanda suke aiki a shago ko yaran kanti a kasuwanni da kuma ‘yan fansho; yaya za a yi da su? Domin kuwa, dukkaninsu ba sa cikin wannan tsarin.

“Haka nan, wadanda ba su da aikin yi kwata-kwata, su kuma waye zai kara musu nasu albashin duk dai da cewa, ba sa aiki; amma ya zama wajibi a yi la’akari da su, dalili kuwa suna so su ci abinci, sabulun wanka da wanki, kudin da za su yi amfani da shi wajen yawon neman aiki da sauran makamantansu, shi yasa na ce; gwamati da ‘yan kwadagon dukkaninsu suna wasa da hankalin ‘yan Nijeriya ne.

“Har ila yau, mene ne zai sa gwamnati har sai ta jira kungiyar kwadago ta je ta rufe tashoshin jiragen sama, bankuna, kasuwanni, masana’antu, ma’aikatun gwamnati da sauransu? Idan aka duba, asarar nawa aka tafka sakamakon rufe wadannan gurare da aka na kwana biyu? Ina da yakinin cewa, ko gwamnatin ba ta san adadin asarar da aka tafka ba.”

Ya kara da cewa, “Tun da shugaban kasa ya san Naira 60,000 yake son karawa a matsayin mafi karacin albashi, me ya sa bai kira ‘yan kwadagon sun zauna shi da su ya baje musu a faifai cewa, ga abin da zai iya biya; amma su yaya suke gani ba? Watakila da an yi haka, da tuni an wuce wajen, amma sai aka buge da cewa minista ya kai masa rahoton da shi da wata fa’ida, illa kawai bata lokaci.

“Maganar da ake yi a halin yanzu, babu wanda ya san inda aka kwana kan batun sulhu da aka yi tsakanin gwamnatin tarayyar da ‘yan kwadagon, domin kuwa ba su fito sun fada wa ‘yan Nijeriya karin da gwamnatin tarayyar ta ce za ta yi a kan Naira 60,000 din ba, sai maganar cewa wadannan bangarorin guda uku za su ci gaba da tattauna.”

“Sau da dama, idan ‘yan kungiyar kwadago sun yunkuro da batun wannan yajin aiki, sai a ce shugaban majalisar dattijai ya kira su ya tattauna da su; daga nan kuma sai ka ji shiru, amma tun yaushe ake ta faman yin abu daya; wata nawa ana kai komo a kan wannan batu na mafi karancin albashi?

Don haka, “ni abin da na fuskanta kawai shi ne, batun wannan sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan kwadago; zancen banza ne, domin kuwa bayan mako dayan da suka dauka za a yi ja-in-ja ne; daga karshe gwamnati ta kai abin yadda har sai mutane sun gaji, sai su ce da ‘yan kwadago ku je kawai duk abin da aka yi mun yarda, mutane su dawo su ci gaba da rayuwarsu; amma magana ta gaskiya, ‘yan kwadago da gwamnatin dukkaninsu ba sa nufin ‘yan Nijeriya da alhairi; wannan ita ce magana ta gaskiya.” In ji shi.

Biyan Albashin Da ‘Yan Kwadago Ke Nema Na Iya Durkusar Da Nijeriya – Gwamnati
Fadar shugaban kasa ta nuna rashin amincewa da bukatar kungiyar kwadago na neman karin mafi karancin albashi na naira 494,000, inda ta yi gargadin cewa hakan zai durkusar da tattalin arzikin Nijeriya.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ne ya bayyana irin illar da hakan zai iya haifar yayin wata hira a gidan talabijin na TBC, yana mai jaddada cewa irin wannan karawar zai tilasta wa kananan ‘yan kasuwa da dama rufe, wanda hakan zai kara ta’azzara rashin aikin yi da tabarbarewar tattalin arziki.

Ngelale ya kara da cewa shirin karin albashin da ake shirin yi wanda ya ninka kusan sau 20 a matsayin mafi karancin albashi a halin yanzu, zai dora wa kananan ‘yan kasuwa wani nauyi da ba zai dore ba, wanda hakan zai haifar da rufewar kamfanoni da kuma asarar ayyukan yi.

Kungiyoyin kwadagon Nijeriya da TUC sun gudanar da yajin aikin na kwanaki biyu a fadin kasar sakamakon kin amincewar da kudin da gwamnatin tarayya ta ce za ta biya na mafi karanci na naira 60,000.
Dangane da irin yadda yajin aikin ya gudana a sassan kasar nan kuwa, wakilanmu sun duba mana lamarin a jihohinsu.

Kano: Yadda Kasuwar ‘Yan Garuwa Da Masu Cajin Waya Ta Bude
Batun yajin aikin da kungiyar kwadagon Nijeriya ta yi na kwanaki biyu a jere, ya haifar da shiga halin tsaka-mai-wuya ga al’ummar Jihar Kano, domin kuwa sun tsinci kansu a cikin duhu ta bangarori da daban-daban.
Yajin aikin da aka fara ranar Litinin da ta gabata, ya jefa dubban mutane cikin halin tsaka mai wuya, musamman batun karancin ruwan sha wanda daukewar hasken wutar lantarki ya haifar.

Mutane da dama sun koka a kan matsalar karancin ruwa wanda ya zama wata gagarumar matsala tare da bude kasuwar ‘yan Garuwa da kuma masu Cajin waya, inda ‘yan Garuwar suka rika sayar da jarkar ruwa guda a kan Nairá 100 zuwa 150, yayin kuma da masu cajin waya suka mayar da cajin kowace waga guda daya kan Naira 100 ko ta cika ko ba ta cika ba.

Batun yajin aikin ya yi kokarin tsayar abubuwa da dama tare da yin sanadiyyar tashin gwauron zabon kayayyakin amfanin yau da kullum. Haka nan, su ma kamfanoni a rukunin masana’antu na Sharada, Chalawa da wani yanki na Bompai, daukewar hasken wutar lantarki ya sanya wasu kamfanoni rufewa baki-daya tare da rage lokutan aikinsu.
Haka lamarin yake a bangaren masu sana’ar sayarwa tare da samar da ruwan sanyi, wanda aka aka rika sayar da kowace ledar pure water a kan Nairá 20 zuwa 30.

Sakamakon wannan yajin aiki kamar yadda idanunmu ya nuna mana, ya shafi ma’aikatun gwamnati da kuma bankuna, yayin da kungiyar likitoci da masu makarantu masu zaman kansu suka yi fatali da shiga wannan yajin aiki, a wasu bangarorin kuma an hangi gidajen mai a kulle.

Kaduna: Marasa Lafiya Sun Shiga Cikin Mawuyacin Hali A Kaduna
Biyo bayan shiga yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka yi na kwanaki biyu, yajin aikin ya jefa marasa lafiya cikin wani mawuyacin hali a Jihar Kaduna, duba da yadda daukacin asibitocin gwamnati suka kasance a rufe.
Lokacin da wakilinmu ya kai ziyara wasu asibitocin gwamnati, ya tarar da duk ma’aikatan lafiya sun shiga wannan yajin aiki, inda hakan ya kawo gagarumar matsala ga yadda asibitoci ke gudanar da ayyukansu.

Wani likita da ke aiki a asibitin Barau Dikko da ke Kaduna, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, “Wannan yajin aiki ya jefa marasa lafiya cikin mawuyacin hali, saboda rashin kulawa, sannan kuma akwai marasa lafiya da dama da suka tagayyara.”

Su ma makarantu a wannan rana, duk sun kasance a rufe sakamakon yajin aikin, wanda hakan ya tilasta wa yara zama a gidajen iyayensu duk kuwa da cewa; wasu sun fara jarrabawa.
Lamarin da ya gurgunta komai, ya sa an bar yara kara-zube a gidajen iyayensu kasancewar wasu manyan makarantu na rubuta jarrabawar karshe na kammala karatun sakandire.

Duk da cewa, babu wani rahoto a gwamnatance na rasa rayukan masu jinya, amma dai an samu gagarumar matsalar wadda ta kai ga har sai da al’ummar jihar suka koka matuka, musamman ganin yadda likitoci da kansu suke ba su shawarar su nemi asibiti masu zaman kansu, domin kai ‘yan’uwansu majinyata; in har suna bukatar ceto rayuwarsu kamar yadda wakilinmu ya tabbatar a asibitocin koyarwa na Barau Dikko da na Yusuf Dan Tsoho.

Abuja: Al’amura Sun Yamutse Sakamakon Yajin Aiki A Ma’aikatu
Yajin aikin da kungiyar kwadago ta shiga a wannan mako da muke ciki na tsawon kwanaki biyu, ya yi sanadiyyar tafka asarar a Abuja.
Wakilin LEADERSHIP, wanda ya je ofishin shugaban ma’aikata na kasa ya bayar da rahoton cewa, da misalin karfe 9:00 na safe ‘yan kungiyar kwadago sun tare babbar kofar da ake shiga ofishin tare da hana ma’aikata shiga domin gudanar da ayyukansu.

Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnatin Nijeriya, Kwamared Ahmed Sylbester Abba ya bayyana cewa, wajibi ne bin dokar wannan yajin aiki.
Kwamared ya kara da cewa, dole ne gwamnatin tarayya ta biya ma’aikata albashin da zai ishe su rayuwa, musamman ma idan aka yi la’akari da yadda rayuwa take kara yin tsada, farashin kaya kuma yake kara ta’azzara a wannan kasa.
Ya ce, “Idan ka zagaya za ka ga dukkanin kofofin shiga wannan ofis a kulle, don haka bukatarmu yanzu ba ta wuce a rika ba mu albashin da zai ishe mu tafiyar da rayuwarmu ba, ganin yadda rayuwa ta canza sanadiyar tsadar da kaya suka yi a halin yanzu.

“’Yan Nijeriya kaf yanzu kansu a hade yake, dangane da wannan lamari, domin kuwa baa bin da ya shafi ‘yan kungiyar kwadago ba ne su kadai, gwagwarmaya ce ta talakawa da sauran masu neman hakkinsu.
“Ko shakka babu, wannan ya nuna cewa kan ‘yan Nijeriya ya kara haduwa kamar yadda suka saba yi a baya, sannan ana sa ran wannan gwamnati za ta saurari kukan al’umma tare kuma da daukar matakin da ya dace, don kawo karshen yajin aikin”, in ji shi.
Haka nan, sakatariyar gwamnatin tarayya, ma’aikatar kudi da kuma bankuna; duk a rufe suke sakamakon wannan yajin aiki.

Adamawa: Bai Kamata NLC Ta Shiga Yajin Aiki Ba – Jama’a
Wannan dambarwa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago kan biyan mafi karancin albashi, ya yi matukar jan hankali tare da raba kan kawunan ‘yan Nijeriya, inda wasu ke ganin wannan yajin aiki a matsayin wanda shi kadai ne zai iya tilasta wa gwamnati biyan wannan mafi karancin albashi, yayin da wasu kuma ke ganin yajin aikin ba zai taba zama mafita ba.

Muhammad Hassan Oska, mazaunin Yola ya ce, “a ganina sam bai kamata kungiyar kwadago ta shiga wannan yajin aikin ba, abin da da ya kamata ta yi shi ne; tsayawa tsayin daka don ganin gwamnati ta tsayar da farashin kayayyaki (Price Control).
“Idan aka yi wa ma’aikata karin albashi, kaya za su yi tsadar da ba a taba irinta ba, yanzu ana sayen buhun masara 75,000 a Adamawa, idan an kara wa ma’aikata albashi; sai an sayi masara Naira dubu dari biyu (200,000),” in ji Oska.

Haka nan, shi ma Umar Sabo ya bayyana cewa, “a nawa ra’yin shiga yajin aikin da kungiyar kwadago ta yi shi ne kadai mafita, domin gwamnatin Nijeriya babu yaren da ta sani idan ba yajin aiki ba, don haka ina goyon bayan kungiyar kwadago kan shiga wannan yajin aiki da ta yi”.

Bauchi: Lamarin Ya Fi Shafar Masu Kananan Sana’o’i, Jama’a Sun Tafka Asara
A Jihar Bauchi ma haka zancen yake, domin kuwa al’umma jihar sun tafka asarar miliyoyin Nairori a kwanaki biyun da aka shiga wannan yajin aiki na ‘yan kwadago. Lamarin dai ya fi shafar masu kananan sana’o’i.
Ibrahim Isa Adamu, wani mazaunin Bauchi, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Babu wanda zai iya kiyasta maka adadin asarar da muka tafka a sakamakon wannan yajin aiki. Misali, akwai mata masu kai abinci zuwa ma’aikatu; sun shirya kamar yadda suka saba, wasu kan yi miya ko soya nama na tsawon kwanaki, sai ga wannan yajin aiki ya kunno kai, sannan kuma babu wutar lantarki; wannan dalili ya sanya su yin asara duba da yanayin zafi da ake ciki a halin yanzu.

“Sannan, masu sana’ar kayan ruwa da ‘yan kasuwa da dama sun yi asara, sakamakon daukewar wutar lantarki wanda wannan yajin aiki ya haifar. Sannan, ‘yan acaba ma sun koka kwarai da rashin ciniki saboda zirga-zirga ta tsaya cak. Asarar da aka yi kawai a bangaren sufuri ba karama ba ce, domin motocin Yankari ma sun shiga wannan yajin aiki.”

“Gaskiya an samu asarar miliyoyin Nairori a Jihar Bauchi cikin wadannan kwanaki biyu kacal. Muna fatan za a samu mafita mai daurewa kan wannan lamari. Haka zalika, a gaskiya halin kuncin da ake ciki yanzu ne ya sa jama’a suka jikata kwarai da gaske, wallahi wasu sai sun fita sun nema suke samun abin da za su ci, wasu kuma neman nasun ya danganta da ma’aikatun da suke aiki, wani kaya yake sayarwa a kusa da wata ma’aikata,” Ibrahim ya shaida.

Kebbi: Na Ya Asarar Abinci Na Kimanin 165,000- Mai Sayar Da Abinci
Jihar Kebbi ma ba a bar ta a baya ba, domin kuwa ta shiga wannan yajin aiki na ‘yan kwadago, don neman gwamnati ta kara wa ma’aikata albashi tare da janye karin wutar lantarki.
Yayin shiga yajin aikin, a Jihar Kebbi masu dakunan sayar da abinci a ma’aikatun gwamnati, sun koka kwarai kan shiga yajin aikin. Domin da yawansu a ranar wannan Litinin din sun riga sun dafa abinci da zimma sayar da shi ga ma’aikata kamar yadda suka saba, amma hakan bai samu ba.

Wakilinmu ya samu zantawa da wata Mai sayar da abinci a bakin sakatariyar ma’aikata da ke gwadangaji, wadda ta nemi a sakaye sunanta inda ta ce, “Sakamakon shiga wannan yajin aiki; na yi asarar abinci na Naira 165,000, wanda ya hada da shinkafa, wake, doya, nama da kifi da sauran makamantansu”, in ji ta.

Shi ma wani mai kayan tireda ya bayyana cewa, “a duk wuni ina yin cinikin akalla Naira 100,000 zuwa 150,000, amma sakamakon wannan yajin aiki da aka shiga, ban iya yin cinikin ko sisi ba, wanda da wannan ciniki ne da nake ciyar da iyalina, duk da cewa tiredar ba dukiyata ba ce; ta maigina ce da ake yin lissafi duk shekara”, in ji shi.

People are also reading