RUƊANIN SARAUTAR KANO: ‘Har yau kotu ba ta damƙa mana takardar dakatar da soke masarautu ko naɗi ba’ – Gwamnantin Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa har zuwa ranar Asabar ba a damƙa mata takardar umarnin dakatar da rushe masarautu da naɗin Sarki Muhammadu Sanusi II ba.
Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Haruna Isah-Dederi ne ya bayyana haka, kamar yadda rahotanni suka wallafa.
Gidan Radiyon Dala FM da ke Kano ya ruwaito a ranar Asabar Dederi ya na cewa, “Da an damƙa wa Gwamnatin Jihar Kano takardar, to shi ne zai fara sani, domin shi ne za a damƙa ta a gare shi, a matsayin sa na Kwamishinan Shari’a, kuma Antoni Janar na Jihar Kano.”
Idan ba a manta ba, Gwamna Abba a lokacin damƙa wa Sarki Muhammadu Sanusi II takardar shaidar kama mulki, ya yi zargin cewa a cikin dare ranar Alhamis aka shigar da ƙara, kuma a lokacin Mai Shari’a wanda ya bada umarnin ya na Amurka.
Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam ya ce a Kano Sarki Muhammadu Sanusi II shi ne Sarki, babu wani da ya isa daga waje ya zo ya canja.