Home Back

Fadace-Fadacen Daba A Birnin Kano: Ina Mafita?

leadership.ng 2024/5/4
Fadace-Fadacen Daba A Birnin Kano: Ina Mafita?

Rikicin Daba a cikin birnin Kano da wasu gefunan birnin ba sabon abu ba ne, za mu iya cewa abu ne da ya ki ci ya ki cinyewa, wato matsala ce ta shekara da shekaru, wanda sanadiyyar hakan rayukan al’ummomi sun salwanta, kama daga ‘yan ba ruwa na da Dukiyoyi jama’a. A inda a wasu lokutan hatta Hukumomin Tsaro ba su tsira daga farmakin rasa rai ba.

Wannan muguwar dabi’a ta Daba zuwa yanzu dai tana son ta zamo kamar wutar daji duba da yadda kullum take ta samun guraben zama a ciki da kauyukan Kano, duk da hukumomin tsaro suna ta ikirarin magance matsalar, da dai-daikun kungiyoyin sakai.

Babban Abun tashin hankali shi ne yadda unguwanni da dama za ka ga yadda suke kokarin kafa kungiyoyin Sa-kai dan tunkara ko kuma magance matsalar tsaro daga tushe amma har zuwa yanzu babu wani kyakkyawan sakamako, in muka iy la’akari da yadda Dabar ke kara bunkasa tare da canja salo a Jihar ta Kano da kuma samun guraben zama.

Mafuta: Akwai Bukatar Duk wata unguwa da suke fuskantar irin wannan matsalolin na tsaro da su tashi su yi aiki tuKuru wajen shigo da kowa cikin aikin samar da tsaro Kama daga kan Masu unguwanni, Limamai, Malamai Na Addini da ‘yan takarda da Kungiyoyin Matasa da na dalibai har da dai-dai kun jama’ar unguwa ko yanki. Domin tsaro na kowa ne, duk inda aka rasa tsaro to lallai za a rasa Aminci da walwala a wannan guri. Haka kuma dole sai an rufe Ido tare da tursasa wa dai-daikun mutanen da za su kawo tasgaro a cikin tsarin ta fuskar alakarsu da yaran da suke aikata wannan dabi’u. Haka kuma sai an yaki miyagun kwayoyi tare da saka idanuwa a shagunan sayar da magunguna.

Sannan a yi kokarin ba wa masu sana’a a kan hanyoyin shige da ficen jama’a wani horo da za su na saka idanuwa kan shige da ficen bakin fuska a kowanne yanki, tare da ba da bayanan sirri na faruwar duk wani motsi ko abu wanda zai kai ga barazana da rayuwa ko salwantar Dukiyoyi.

Abun Lura: Dole Yayin Gudanar Da Wannan Aiki Sai An cire
1). Tsoro: Kowa ya ji cewa rai daya yake zai iya badawa wajen tunkarar yaran da suke hana iyaye, kanne, maza da mata da kasuwancin unguwa zaman lafiya, uwa uba gudanar da ibadoji, tare da tunkarar kalubale kan iyayen yaran da za su ki bada hadinkai kasancewar ‘yayansu ne ko kanne ko yayye ke aikata wadannan ayyukan na ta’addanci a unguwanni.
2). Wariya: Wato cewa ni ai bai shafe ni ba sai a bar wa wane da wane.
3). Bangaranci: Ma’ana ai ni ba a yi a yankin da nake ba, to ka sani tsaro na kowa ne.
Allah Ka amintar da Unguwanninmu, da garuruwanmu ka ba mu lafiya da zama lafiya.

People are also reading