Home Back

Labarin Wasanni: Jamus ta haye

dw.com 2024/7/7
Euro 2024 | Jamus | Switzerland
Jamus ta sha da kyar a hannun Switzerland, ko da yake ta haye zuwa zagaye na biyu

.

A gasar neman cin kofin kasashen Turai da Jamus take daukan nauyi, mai masaukin bakin jiya Lahadi ta tashi 1 da 1 jiya a wasan da ta fafata da kasar Switzerland, inda aka yi kare jini biri jini. Kasar Switzerland ta fara jefa kwallo a ragar Jamus ana mintoci 28 da fara wasa, inda Jamus ta rama da kyar bayan karin bmintoci biyu da aka yi ana kokarin tashi. Tun farko Jamus ta lashe wasannin biyu da ta kara abin da ya ba ta damar tsallakawa zuwa gagaye na biyu. Haka a jiya Lahadin Hangari ta doke Scotland daya ya nema. Yanzu haka dai kasashen na Jamus da Switzerland suka tsallaka zuwa gazaye na biyu daga wannan rukuni na A. Ita dai Jamus ta kasance a matsayi na farko a wannan rukuni na A. Sannan da yammacin wannan Litinin a rukunin na biyu na B, Albaniya za ta kece raini da Spain, kana kasar Koroshiya za ta fafata da Italiya, inda daga ciki za a smau kasashe biyu da za su tsallaka zuwa gazaye na biyu. A  Talatar da ke tafe kuwa: A wasannin farko na lokaci guda na rukunin D: Faransa za ta fafata da Poland, yayin da Netherland za ta kece raini da Austiriya. Kana a rukuni na C, kasashen Denmark da Sabiya za su fuskanci juna haka ita ma Ingila za ta fafata da Slovaniya. Daga ranar Asabar mai zuwa ake fara wasannin na zagaye na biyu na neman cin kofin kasashen Tutai da Jamus take daukan nauyin.

Ana sa ran Jannik Sinner dan kasar Italiya ya taka rawar azo a gani lokacin gasar tennis ta Wimbledom da ake fara daga ranar Litinin mai zuwa 1 ga watan gobe na Yuli har zuwa 14 ga watan na Yuli. Wannan gasa tana cikin masu tasiri na tennis da ake karawa tsakanin shahararrun 'yan wasan tennis na duniya duk shekara. Dan shekaru 22 da haihuwa Jannik Sinner tagomashinsa na tashi inda kowani lokaci yake kara yin sama a jerin gwanayen wasan na tennis da ake fitarwa, tun lokacin da ya lashe gasar Australiya Open da aka gudanar a farkon wannan shekara ta 2024.

A karshe, Donia Abu Taleb 'yar kasar Saudiyya ta zama mace ta farko daga kasar da ta tsallaka zuwa wasan damben Taekwando na wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya, Olympic da birnin Paris na Faransa zai dauki nauyi. 'Yar shekaru 27 da haihuwa Donia Abu Taleb ta fuskanci kalubale da dama da suka hada da samun horo tare da maza saboda babu matan da suke wasan na Taekwando a kasar kuma tana fatar ganin ta samo lambar zinare na farko ga kasar ta Saudiyya, lokacin wasdannin na birnin Paris. Yanzu haka dai hukumomin Saudiyya na karfafa gwiwar mata shiga a dama da su a fannonin wasanni, a kasar ta yi suna wajen bin ra'ayin mazan jiya da aiwatar da hukunci karkashin tsauraran dokokin addinin Islama.

People are also reading